HUKUNCIN DILLANCIN AURE

HUKUNCIN DILLANCIN AURE


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum,
Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure?  
:
*AMSA*👇
:                                
Wa'alaykumussalam, Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi S.A.W yake cewa: "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun yi saɓani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da yaje neman aure :

1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai.

2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura. Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki:

1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.

2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba , a facebook, ko a jarida.

3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.

4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.

Allah shi ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.


Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)