*ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALA BA ?*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum. Tambayata Anan shine:. Menene hukuncin yin wankan janaba batare da yin alwala ba?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar yadda ya zo a hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi S,A.W. ya siffanta mata wankan janaba da cewa: "Ya ishe ki, ki zuba ruwa sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in kika yi haka, kin tsarkaka" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lam bat a: 251.
A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya nuna wankan ya yi da waccar sifar da kika tambaya.
Saidai sifar da ta zo da alwala a hadisin Nana A'isha ita ce mafi cika, kamar yadda malamai suka bayyana.
Allah ne mafi sani.
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
6\3\2016