*ZAN IYA RARRABA KAFFARAR RANTSUWA ?*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, Dr. don Allah a amsa mana wannan
tambayar. Ya halatta in raba kaffarar azumin
rantsuwa?
*Amsa*
Wa alaikum assalam,
ya halatta a rarraba azumin
kaffarar rantsuwa, saboda aya ta: 89 a suratul
Ma’ida da ta yi bayanin kaffarar rantsuwa ba ta
kayyade azumi ukun da jerantawa ba, wannan
yasa da yawa daga malamai suka tafi akan
halaccin rarraba azumin.
Ba’a yin azumi uku a kaffarar rantsuwa sai ga
wanda ya kasa ciyar da miskinai goma ko tufatar
da su, kamar yadda ayar ta yi bayani dalla-dalla
akan haka.
Allah ne mafi sani
*Dr, Jamilu Zarewa*
1/01/2017