*WANDA YAKE CIWON IDO, ALWALA ZA TA FADI A KANSA?*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, Mallam Ina da
tambaya?
Idan mutum aka yi masa aiki a ido
an ce kada ruwa ya taba, to, idan zai yi sallah
Taimama zai yi ko zai iya yin alwala ba tare da
sa ruwa a wajen ba? Allah ya saka da alkhairi.
*Amsa*
Wa Alaikum Assalam,
Zai yi alwala cikakkiya, sai ya tsallake wurin da yake da
ciwon, saboda Ka’idar : ﺍﻟﻤﻴﺴﻮﺭ ﻻ ﻳﺴﻘﻂ ﺑﺎﻟﻤﻌﺴﻮﺭ
Duk ibadar da za a iya yin wani bangarenta, to,
dukkanta ba ya saraya, saboda rashin iya aikata
wani bangarenta, sai fa idan bangaren na ta,
shari’a ba ta bukatarsa, kamar mai olsar da zai
iya yin azumi zuwa Azahar ya sare.
Allah ne mafi sani
21/12/2016
*Dr. Jamilu Zarewa*