MATA KU FARKA 😊

MATA KU FARKA 😊






MATA IYAYEN GIDA......





Ba ko wacce mace take karbar wannan kirarin ba sai wacce tai hakuri da juriya a cikin gidan Auren ta.

Yanzu rayuwa ta canza tattalin arzikin Al'ummah dada kasa yake, bukatun da magidanci yakan iya magancewa a cikin gidan sa ada yanzu ba lallai ya iya maganin su ba.

Ya! Ke yar uwa kiyi hakuri da abinda ya samu, ki yi tattalin sa da iya bukatar da ta zama dole a cikin gidan ki.

Kaso mafi yawa daga matsalolin gidan Aure suna faruwa ne daga rashin fuskanta a tsakanin Mace da Miji. 

Matsalar gidan Auren ki ba lallai itace matsalar gidan Auren wata ba, kin ga kuwa zaman lafiyar ki ya ta'allaka da samun daidaito tsakanin ki da mijin ki domin warware matsalar ku.

 Kiyi Hakuri !
 Kiyi Addua !!
 Kiyi hakuri !!!

  In Sha Allahu gidan ki zai cika da haske😊

Ya! Ubangiji ka kawo mafita ga matar data mika dukkanin lamuran ta gare ka AMEEN 🤲.
Post a Comment (0)