HUKUNCIN KARBAR HAYAR DA ZATA KAI GA MALLAKAR ABU

*_HUKUNCIN KARBAR HAYAR DA ZA TA KAI GA MALLAKAR ABU_*

                               *Tambaya*
Assalamu alaikum.
Menene hukuncin shari'a akan irin yanda mutane suke yi, na sayan abin hawa su bawa direba da sharadin cewa : a kullum zai kawo wani ayyanannen kudi (kamar N500), har na zuwa tsawon kamar shekara, akan cewa idan ya shekara yana kawowa  abin hawan ya zamo na sa.

                                    *Amsa*
Wa'alaikumus Salam, To dan'uwa wannan ciniki daga baya ya shigo cikin kasashe musulmai, amma malamai magabata ba su san shi ba, saboda da can a kasashen turawa aka san shi, don haka malaman wannan zamanin suka yi sabani akan wannan mas'alar, akwai wadanda suka halatta wasu bangarori na wannan mua'amala, saidai fatawar manyan malaman Saudiyya da kuma kwamitin fatawa na din-dai-din ita ce: haramta wannan nau'i na haya kamar yadda suka tabbatar da hakan a zamansu na ranar:29/10/1420 saboda ya kunshi zalunci, domin zai iya yiwuwa, mutum ya sare kafin ya kai lokacin da aka diba masa, ka ga kudin da ya biya a baya, ba zai ci gajiyarsu ba, sannan ciniki biyu ne cikin ciniki, don haka ya haramta, kuma hanya ce da za ta jawo talakawa su dinga cin bashi, ba tare da sun damu ba.

Allah ne ma fi sani.

6/4/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)