YA HALATTA IN KIRA SHEHU IDAN WANI ABU YA FARU DA NI?

*YA HALATTA NAKIRA SHEHU, AYAYINDA WANI ABU YA FARU DANI ??* : Daga zauren Khulafa'ur-rashiidun : Assalam alaykum malja'afar tan kananan lfy tby ta itace dan ALLAH dadama idan wani abun tsautsayi zaisameni nakira sunan wani mutum ba ALLAH ba kamar wani waliyyi ko kuma makamancin haka ALLAH ya bada ikon amsawa : ***** : Wa alaikumussalam To bawan ALLAH, gaskiya qur'ani da sunnah suna zargin duk me aikya haka da mummunan zunubin shirka! Kuma mutum ya mutu akan haka, gaskiya shiga aljannah zemar wuyaa!! Domin ALLAH yasanar damu idan masifa tazo ko bal'ie to muce "innalillahi wa illa ilaihi raji'un" kaman yadda bayani yazo asuratul baqara!! Amma ayayinda muke kiran wanin ALLAH tofa, munta6e, domin shi waliyi ko wani salihin bawa, bashi ya halicci kansaba, ALLAH ne ya halicceshi. . kuma dayawa daga cikin wadan da ake kiransu. Matattune, idan har zasu iya amfanan kansu, symudawi da rayuwan sumana "suma su riqa yawo Aduniya kaman yadda rayayyu sukeyi, to amma dan anunama basa iya amfanar kansu da kansu, shiyasa suke mutuwa, alokcinda suke kan jin dadin rayuwa! Lokacin da sukeso su qara shekara dayawa, se mutuwa ko jinya ta bigesu, su gagara amfanar kansu;- masu riqan wanin ALLAH ko kuwa musulmai ne ko mala'ika ko annabi ko salihan bayi, duk laipi ne, matuqar abind suka roqa ALLAH ne kadai keda ikon yi:- misali a " zaka fadi wani yana gefen ka zaka iya riqeshi, ko kace wane riqeni zan fada" amma ba kowa agefenka, seka kira wani wanda yake chan wata qasa ko wani gari ko wata unguwa koma yana cikin qabari, kana me neman taimakon sa!! Ai kayi shirka anan!!! ALLAH ya hanamu yin haka:- Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya." (Ahaqaf 4) ( وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّن يَدْعُو مِن دُونِ اللَّهِ مَن لَّا يَسْتَجِيبُ لَهُ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَهُمْ عَن دُعَائِهِمْ غَافِلُونَ ) Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin ALLAH wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhali su (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu? الأحقاف (5) Al-Ahqaf Wannan zargine da ALLAH ta'ala yakeyiwa duk wani mutumin dayake kiran wanin ALLAH! Dan haka gaskiya kiran wanin ALLAH haramun ne cikin Qur'ani da hadisi abisa fahintan malaman farko, dan haka gaskiya muguji yiwa ALLAH shirka, dan wanda muke kira ba'abunda suka ta6a halitta, barimadai halittansu akayi:- "Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "ALLAH ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin ALLAH ne, idan ALLAH Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata ALLAH ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara." (suratul zumarzumar 38). = Inmuka yadda dukkan masifa daga ALLAH take se mu zauna lapiya, ta hanyan neman kariya awajen ALLAH :- . "Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga ALLAH, mai sauƙi ne." (Suratul hadid 22) . Muyi hakuri mubi saukin da ALLAH yamana, seta kaimu ga shiga aljannah, amma tabbas kachigaba da kiran wanin ALLAH ka mutu akan haka, tofa hanzari ya qare, ALLAH yakiyayemu dayiwa ALLAH shirka qarama ko babbba! Wallahu a,alam . ➡Muhammad Auwal Hussain Abu ja'afar ======================== *```Date* ```[28-06-1439]Hj {16-03-2018} _Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_ +2347035269582 +2348063796175 +2349033206238 *```Kuna iya samun mu ta facebook*``` facebook.com/khulafaurrashidun ((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ)) 〰〰〰〰〰〰〰〰✔ Aji Tsoron ALLAH kada achanja mana komai! In anga kuskure asanar damu !
Post a Comment (0)