🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
🤥 Kullun kina kallon matan da suka fiki, amma kin kasa godewa Allah cewa ke kina gaba da wasu, kuma kina cikin irin ni’imar da Allah ke son ki da ita..ni’imar ci, da sha, da lafiya, har da aure. Wasu ma basu yi ba.
🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
🌹 Idan za ai maki abokiyar zama (kishiya) ko za ayi wa ýarki ko kanwarki ko mahaifiyar ki..sai hankalinki ya tashi!!! ba kyaso.
Amma ɗan ki, wanki, ko Qaninki, idan zai Qara aure.. Ke ce Qirjin biki..da murna da muzguna ma matarshi..
🙄 *A SAKE TUNANI!!!*
💏 Kullun kina son kiga mijinki yana kula da ke yana kyautata maki, ko mijin ýarki, amma ba kya son kiga ɗan uwanki yana kyautata wa matarsa.
🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
🏚 Kullun kina son ki zauna lfy a gidanki, amma matar ɗan uwanki kin sa mata ido, idan tayi kuskure kamar a kanta a ka fara;
idan tayi alkhairi, kice tayi barna,
idan tayi tattali kice tayi rowa,
Idan tayi marhaba kice ta faye surutu, idan tayi shiru kice bata da fara’a..
Mata ayi a hankali..
🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
❌ Idan aka saki kishiyar ki ko ta mutu! Ki na ta murna kamar mutuwa bata kowace ba.. kamar qaddarar saki bata bisa kan kowa, ki yi ta cutar da yaranta..
kina ka sa tunawa cewa kema hakan zai iya faruwa da ke.. mutuwar ma rigar kowa ce.
🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
🌷 Kullun kina son kiga ýaýanki sun shiryu, amma kina son na wata su lallace su tagaiyara. Kullum zancen ki na dan wani ko yar wani ta shiga wani hali ne.. Qaddarar kowa bata wuce shi!
🤔 *A SAKE TUNANI!!!*
🗂 Idan kika karanta wannan saqon za ki yarda dani cewa haka halin WASU matan da yawa daga cikin mu ya ke. Kuma ba sa son a gyara musu ko a jawo hankalin su da su gyara.. Kar a daina yi musu fadakarwa da wa’azi, a ci gaba da yi.. idan ma basu yi ladama ba, lokaci babu abunda ya bari..
wani abin zasu tsinci kansu a cikin sa tsundum.. dole wata rana zasuyi da na sani.
🤔 *A YI YAQI DA SHAIDAN A SAKE TUNANI!!!*
*```Allah ya shirye mu, ya azurta mu da zuciya mai adalci da karfin imani..ya ba mu ikon SAKE TUNANI ya sa mu gama lfy.``*
Amin