AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //03

AƘIDUN SHI'A DA TA'ADDANCINSU A TSAWON TARIHI //03


WALLAFAR: Malam Najeeb ElKabir Kwarbai

MAGANGANUN MALAMAI A KAN ABDULLAHI ƊAN SABA'I.

● Ibnu khaldum Yana cewa: “Lallai Abdullahi ɗan Saba'i shi ne wanda aka sanshi da suna Ibnu Saudah, ya kasance bayahude ne, ya yi hijira a lokacin mulkin Usman, baibkyautata Musuluncinsa ba... [Tarikhu Ibnu Khaldum 2/139]

● Albagdadi Yana cewa: “Ibnu Saudah ya kasance asalinsa bayahude ne daga mutanen garin Alhiratu, ya bayyanar da Musulunci kuma ya nemi ya sami karɓuwa a wajen mutanen Kufa, ya ce musu: “Lallai ya duba Attaurah ya ga cewa kowane Annabi yana da wasiyyi, saboda haka Aliyu shi ne Wasiyyin Muhammad (SAW), kuma shi ne mafi alherin Wasiyyi, kamar yadda Muhammad (SAW) shi ne mafi alherin Annabawa.... [Duba: Alfarƙu Bainal Firaƙ 225, bugun Darul Afaƙ Al-jafid, Beirut]

● Ibnu Hazmin Yana cewa: “Sababin korar da Aliyu ya yi masa zai bayyana a garemu, cewa shi ne farkon ɗan bidi'a a Musulunci. Yana cewa; “Abdullahi ɗan Saba'i Alhumairiy wanda ya cewa Aliyu “Kai ne! Kai ne! Kai ne!” Ma'ana “Kai ne Allah”, sai (Aliyu) ya kore shi zuwa wasu garuruwa. Ya kasance Bayahude ne, sai ya Musulunta. Ya kasance a Yahudanci yana cewa Yusha'u ɗan Nuh Wasiyyin Musa ne, sai ya faɗi irin haka fa Aliyu. Shi ne farkon wanda ya fara bayyanar da imamancin Aliyu, daga gareshi aka samu ɓullar Ƴan Shi'a Gullat (masu wuce iyaka). Yana cewa lallai Aliyu yana raye ba a kashe shi ba, kuma a tare da shi akwai wani yanki na Allantaka, Shi ne (Aliyu) wanda yake zuwa a cikin girgije, tsawa sautinsa ce, walƙiya kuma wulƙawarsa ne.

Da sannu zai sauƙa a bayan ƙasa ya cika ta da adalci, kamar yadda ta cika da zalunci. Shi ne farkon wanda ya ƙirƙiro TAWAƘƘUF da GAIBAH da RAJA'A. Kuma shi ne ya ƙirƙiro maganar cewa wani yanki na ALLAH yana fita daga jikin Aliyu zuwa ga sauran Imamai a bayan shi. [Duba: Al-Fisal Fil Milal Wal Ahwa'i Wan Nihal 2/11, bugun Darul Muthanna Bagdad]

ƘARIN BAYANI: Abunda ake nufi da waɗannan kalmomi, su ne kamar haka: TAWAƘƘUF shi ne ka yarda cewa Aliyu ne kawai Imami. GAIBAH kuma shi ne imani da cewa duk wani rayayye yana iya ɓacewa a duniya a dena ganin shi na wani lokaci, sannan sai ya dawo. RAJA'A kuma shi ne duk wani mamacin da ya mutu, to zai dawo duniya ya cigaba da rayuwa har ya haifi ƴaƴa.

MAGANGANUN MALAMAN SHI'A A KAN ABDULLAHI ƊAN SABA'I.

● Abu Muhammad Alhassan Bin Musa Bin Muhammad Al-Naubakhatiy Yana cewa: “Jama'a da yawa daga cikin ma'abota ilimi daga cikin mabiya Aliyu (AS) sun haƙaito cewa lallai Abdullahi ɗan Saba'i bayahude ne, sai ya Musulunta, kuma ya rinƙa nuna soyayya ga Aliyu (AS). Ya kasance a lokacin yana bayahude yana cewa Yusha'u ɗan Nuh shi ne Wasiyyi ga Musa (AS), a Musulunci ma sai ya rinƙa faɗar haka, bayan wafatin Annabi (SAW) a kan Aliyu (RA) shi ne farkon wanda ya fara magana akan cewa wajibi ne Aliyu (AS) ya zama imami, kuma shi ne ya bayyanar da barranta ga maƙiyanshi da bayyana waɗanda suka saɓa mishi, kuma ya kafirta su, daga nan ne waɗanda suka saɓa ma Shi'a suka ce asalin Rafidanci (Shi'a) daga Yahudanci aka samo shi. [Duba: “Firaƙu Shi'a 32-34, tahƙiƙin Dr. AbdulMuna'im Alhafniy, bugun Darul Rashad Alƙahira 1992]

● Abu Amru ɗan Umar Bin Abdul'aziz Alkishiyyu Yana cewa: “Bayan ya yi bayani irin wanda Abu Muhammad Alhassan Naubakhtiy ya yi, sai ya kawo ruwayoyi guda biyar waɗanda isnadinsu ya tuƙe zuwa ga imamansu, waɗanda suke nuna barrantarsu da la'antarsu da zarginsu ga Abdullahi ɗan Saba'i. Daga cikin ruwayoyin akwai:

Daga Abiy Ja'afar Ya ce: “Lallai Abdullahi ɗan Saba'i ya kasance yana cewa: “Shi Annabi ne”, kuma yana cewa: “Amirul Muminina (AS) shi ne Allah Maɗaukakin Sarki” (Wa'iyazubillah). Da labari ya kai zuwa ga kunnen Aliyu, sai ya aika aka ƙira shi, aka tambaye shi kuma ya tabbatar da abun da yake faɗa Yace: “Na'am Kai ne! Ya kasance an jefa mani a raina cewa kai Allah ne” Ni kuma “Annabi ne” Sai Amirul Muminina (AS) Ya ce: “Tir da kai! Haƙiƙa Shaiɗan ya yi nasara a kanka, ka dena faɗan wannan maganar, sai ya ƙi, daga nan aka tsare shi har tsawon kwana uku, amma yaƙi ya tuba, sai aka ƙona shi da wuta.

Zamu ci gaba in shaa ALLAH.
Post a Comment (0)