JARUMI SHAH RUKH KHAN YA CECI RAYUWAR MANAJAR JARUMA AISHWARYA


 JARUMI SHAH RUKH KHAN YA CECI RAYUWAR MANAJAR JARUMA AISHWARYA 
 

Kasancewar ranar lahadin da ta gabata ita ce ranar bikin Diwali, Jaruman Bollywood da dama sun shirya tare da caskaÉ—ewa a tarurruka daban-daban a wannan rana. 

Jarumi Amitabh Bachchan ya shirya wani Æ™asaitaccen biki a gidansa mai suna jalsa a wannan rana. Wannan biki ya samu halarta daga manyan Jaruman Bollywood da Æ™ananunsu baki É—aya, cikinsu kuwa har da Jarumi Shah Rukh Khan. 

Sai dai wani abun tsautsayi ya faru a wannan rana, domin kuwa Yayinda ake ci gaba da gudanar da wannan shagali ne wuta ta tashi sakamakon Æ™ananan fitilun aci-bal-bal da aka kunna domin wannan biki. Majiyar Times of India ta ruwaito cewa manajar Jaruma Aishwarya Rai Bachchan wacce suka daÉ—e suna tare mai suna Archana Sadanand ta tsallake rijiya da baya daga wannan wuta da ta tashi, kuma ba kowa bane ya ceto rayuwarta face Jarumi Shah Rukh Khan. 

Rahoton ya Æ™ara da cewa; bujen Archana ne ya kama da wuta sakamakon Æ™ananan fitilun aci-bal-bal da aka kunna domin gudanar da wannan biki. Shah Rukh Khan, wanda a wannan lokaci yana wajen, shi kaÉ—ai ne yayi hanzari wajen ganin ya kashe wutar da rigarsa. Archana dai rahotanni sun bayyana cewa ta samu Æ™una a kaso 15 cikin É—ari na jikinta a hannayenta da kuma Æ™afarta ta dama, shi ma Jarumi Shah Rukh Khan É—in ya samu wasu Æ™ananan raunuku a sakamakon Æ™oÆ™arin kashe wutar da yayi. 

Kamar dai yadda rahotannin suka bayyana, a yanzu haka Archana tana ci gaba da samun kulawa a asibiti, kuma an ajiye ta ne a waje na musamman don gudun kada wasu cututtukan su shiga jikinta ta cikin raunukan da ta samu. 

Majiyar dai ta Æ™ara da cewa, wannan lamari ya faru ne da misalin Ƙarfe uku na dare a cikin gida Jarumi Amitabh Bachchan Yayinda wacce iftila'in ya faÉ—awa take tare da É—iyarta. 

To anan sai mu ce Allaah Ya kiyaye gaba, wacce ta samu rauni kuma Allaah Ya bata lafiya. Shi kuma Jarumi Shah Rukh Khan Allaah Ya saka masa da Alkhairi bisa aikin Æ™warai da ya aikata. Aameen 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 

Post a Comment (0)