LABARI MAI DAƊI GA MASOYAN SHAH RUKH KHAN

*LABARI MAI DADI GA MASOYA SHAH RUKH KHAN*

Gobe biyu ga watan 2 November wadda tayi daidai da ranar cika shekaru 54 a duniya. Sarkin Bollywood Shah Rukh Khan ake sa ran zai kaddamar da Film din da zai fito a gaba. Wadda tuni rade-radi sun karade social media musamman ma kafar sada zumunta ta Twitter wadda suka nuna ce wa an sawa fim din suna #Sanki a yaren Hausa zamu iya cewa Kalmar #Sanki tana nufi Mutum Fusatattace ko mai Taurin Kai. Kamfanin Red Chillies na #Srk da Dharma Productions na Karan Johar zasu dauki nauyi yin film din wadda za'a fara shooting dinsa a December na wannan shekarar. Za'a sake sa a Diwali na 2020.
 A jita-jitar dai an bayyana sunan kwararren mai bada Umarnin nan na Kollywood Atlee Kumar a matsayin wadda zai bada umarnin film din. Shi dai a Atlee ya bada umarnin films guda 4 a masana'antar films ta Kollywood wadda duk suka kasance matakin Blockbusters. Tun watannin baya dai ya bayyana aniyarsa ta fantsamawa sauran masana'antu fina-finai na India inda nuna sha'awarsa akan Bollywood da Tollywood. SRK da Atlee sun fara tattaunawa ne tun a watan April na wannan shekara a lokaci da SRK ya je chennai gani wasan Cricket da team dinsa na Kolkatta Knight Riders zasu buga acan.
In dai haka ta tabbata za mu iya ce wa lokacin farfadowar SRK ta zo bayan dogon suman da yayi ko daga sunan da aka bawa film din za mu iya cewa wannan kalan film din shi yafi dacewa da SRK ba irin su Zero da #JHMS ba. Ina da tabbacin haduwar Atlee da SRK zata ba citta sosai. Ba iya 300cr ba don abu ne mai yiwowa Sarki Bollywood ya bude 400cr da #Sanki 

#DPrince_Pantami

Post a Comment (0)