BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 03


BABAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYAREA

Fitowa ta 003

 Tsaya ka/ki karanta Watakila zai Amfane ka/ki


Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: Annabi Muhammad SAW, ya haramta duk abin da ya haramta saboda dangantaka ta Jini a wajen yin Aure, a dalilin dangantaka ta Shayarwa kuma ya hana a 'hada Mace da 'Yar uwarta ko 'Yar uwar Ubanta.
       Wanda duk ya Auri Mace, toh da zarar an 'daura Auren kafin ya Sadu da ita Matar ta Haramta ga iyayensa da 'ya'yansa, kuma shi ma iyayen sun Haramta a gare shi, 

Amma 'ya'yanta, ita matar, ba za su Haramta gare shi ba Har sai ya Sadu da Uwar Tukuna, ko kuma ya dadi da ita ta hanyar Aure ko Mallaka.
      Halal ba ya haramta saboda Zina, Allah mai tsarki ya Haramta Saduwa da Kafirai wadanda ba Ahlul-kitabi ba ta hanyar Aure ko Mallaka,
       Amma ya halatta a Sadu da Ahlul'kitabi ta Hanyar Mallaka, kuma ya halatta a Sadu da 'ya'yansu ta hanyar Aure, Saduwa da kuyanginsu kuma bai halatta ba ga 'Da ko bawa ya Sadu da su.

Bai Halatta Mace ta auri bawanta ko Bawan danta ba. Haka nan bai Halatta ga Namiji ya Auri kuyangarsa ko kuyangar dansa ba.
       To amma ya Halatta gare shi ya Auri kuyangar Mahaifin sa da kuma kuyangar Mahaufiyar sa. Ya halatta mutum ya Auri 'Yar Matar Baban sa Wadda ba 'Yar Ubansa ba ce, kaman misali Agolan baban ka idan 'yarta ta maka kuma takai Aure ya halatta ka nemeta ka Aura
        Ya Halatta ga 'Da da ya Auri Mata 4 'ya'ya Musulmai ko Ahlul-kitabi, ya halatta ga 'Da idan bai Sami ikon auren diya Mace ba, kuma yana jin tsoron kada yayi Zina da diyar Mutane, ya fada ga halaka, toh ya Auri kuyanga. Ko kuma ya kama yin Azumi kaman yadda Annabi yace.
       Wajibi ne mutum ya ji Tausayin Matar sa, sannan yayi Adalci a tsakanin Matan sa. Ko kuma matar sa idan daya ne. Ciyarwa da wurin zama duk suna kansa gwargwadon ikonsa, ke kuma sai kiji tsoron Allah kada ki ga Mijin kawar ki yana yiwa kawar ki goma sha biyu, gashi Mijin ki baya miki haka, kice dole dole sai Mijin ki ya miki irin abinda wancan Mijin kawar kin yake mata. Duk abinda ya miki komin kankantar shi ki karba kiyimai godiya ki sa masa Albarka kice Allah yasa gobe ma a Kawo irin shi ko fiye da haka, kada ki yadda ko da na minti guda ce kina nuna fushin ki ga Mijin ki akan baya miki kaman yadda akeyiwa wasu matan. Idan kullum kina sawa Mijin ki albarka kuma kullum kina nuna wadatuwar ki gare shi kina faran ta masa ran shi, Dalilin wannan Addu'ar naki indai kullum haka kike yiwa Mijin ki sai ki ga kullum idan yafi Allah na budamai kofofin Samun shi. Amma ya kawo kince bayayi ba. Ko kuma baya miki Alhalin yana iya kokarin sa. sannan ke baki taba ce masa kin gode da irin kokarin da yake yi ba, saboda baya miki irin yadda Masu kudi sukeyiwa matan su. Toh yaya Allah barai jarrabeku da kullum babu ba? Ke kullum kina cikin wahala Mijin ki ma haka. Yadace Kisan me zakiyi ki samu Rahamar Allah a Ranan Alkiyama, bawai kisan me zakiyi duniya ta samu gareki ba.
          Babu rabon kwana ga kuyangar sa ko Ummawaladarsa, babu ciyarwa ta dole ga Mace har sai ya Sadu da ita ko kuma sai an same shi da ita suna tare kuma ta zama Wanda a lokacin za'a iya kwatantawa da har ya iya Saduwa da ita. Kai kuma wajibi ne Gare ka kaji tsoron Allah ka tausaya matar ka a koda yaushe. Ka tallafa matar ka tamkar ka siyo Tomatir Wanda yagama Nuna kuma yana cikin irin kwandon nan ance ka dauko ka sa shi a Daki, yaya zaka yi? 

Shi ne a lokacin zaka gama iya tallafa wannan kwandon saboda kada tomatir din su faffache. Ko kuma kaman misali ace ka siyo kwaiyi dayawa an sa ma su a leda, nasan barakayi garaje wajen ganin ko da guda daya ne ya fashe ba, haka yadace da Shari'a ka tsaya dakyau wajen tausayama Matar ka, 
      Kada kai a waje ka tsaya kanata furta mata abinda idan ta zo gidan ba shi zata tarar ba, kayita mata kariyan cewa zaka kula da ita sosai kaman yadda kai kake kula kanka, kace Kai bara ka taba so ka ga abinda ya taba lafiyarta ba. Ka zo kullum dukan diyar mutane kake yi babu dare babu rana, Annabi Saw yana cewa akan ya dauki Hannun shi ya bugi Matar shi wallahi gara Hannun ya Rube yanke ya yarda shi. Annabi ya fada haka saboda irin tausayawa Matan shi da yake yi. 
     Ina ga kai kuma kullum kana cikin Zunubi, amma baka tausayawa matar ka ko kadan, rabonta da taji ka yabeta ko kwalliyarta ko Girkinta, watakila tun lokacin da ta taba kawoma wani girkin da tayima tun tana gidan su, wannan ba koyarwan Annabi bane, Mazaje yadace gareku idan ka Nunawa Mace so da kauna tun a waje, kuma kai kullum kana cewa idan ta zo gidan ka zaka mata fiye da wannan zaka nuna so da kauna gareta, toh wajibin ka ne ka cika Alkawarin haka indai kana son ka samu tsira a Ranan Alkiyama.
      Ka tsaya dakyau ka tausayawa Matar ka. Misali Idan kaje Hotel na inda ake siyar da Abinci zaka ga wanda ta dafa Tuwon bawai ita ne zata siyar ba, haka Wanda ta kwance tuwon bawai ita ne zata Siyar ba, hakan Wanda ta share wajen saida Abincin bawai fah ita ne zata zauna ta siyar da abincin ba, haka kuma Wanda tayi wanke wanke nan ma bawai ita ne zata siyar ba, haka kuma Wanda zata kaiwa customer abincin bawai ita ne mai siyarwa, harda ma Mai karban kudin.
       Ka duba duk wannan aikin mutane nawa a hotel sune masuyi kuma suce sun gaji, amma gashi Matar ka ita kadai tana yin Aikin fiye da Mutane nawa harda kayan ka sai ta wanke su ta goge, don Allah dan Uwa Idan baka ji tausayinta ba, kayi mata godiya itama taji dadi tasan lallai tana kokari a gidan ba, wacece zaka je kayiwa godiya ko ka tausayawa toh? Gashi kuma a waje hakan kake fada mata kuma kake nuna mata, matukar ka ganta cikin wani dan karamin damuwa hankalin ka yayita tashi kanata nuna damuwar ka, ita kuma tana jin dadin ta samu Wanda zai bata kulawa, amma meyasa tunda a yanzu ta zama mallakin kane baka yin idan kake Nuna mata a waje_____

Ku biyo mu a Fitowa na in Allah ya kaimu.


Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah 
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Mai Tarin Albarka Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Jihar Kai tsaye ta WhatsApp Number namu
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)