BAYANIN AURE DA SAKI DA MAJIƁINTANSU 04


BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I DA SHAYARWA.

Fitowa ta 004.

Ci gaba da bayani daga inda muka tsaya: Auren Tafwidi Halal ne, Tafwidi shine Miji da Mata su yi Aure ba tare da yanke Sadaki ba, wato Miji yace nawa ne kudin Sadakin ki? Toh zasu iya yin Auren su ba tare da an Shirya hakan ba. Amma kuma ba zai Sadu da ita ba har sai ya ba ta Sadakinta ta damke su a hannunta kafin nan ya Sadu ita,
     Sannan Idan ya ba ta Sadakin da ya dace da Matsayinta, toh lallai ne ta karba, idan kuwa ya Kara akan Wanda yadace da ita, toh sai a ba ta zabi, idan ta ce ba ta son sa a yanzu, toh sai a Raba su, sai dai idan ya lallashe ta ta yarda ko kuma ya Kara mata wani Sadakin, to lallai ne ta yarda. Idan wani tsakanin Miji da Mata ya yi Ridda, to sai a warware wannan Auren, amma da Saki za'a warware kada ace ma Matar toh maza tafi gidan ku a yanzu babu Aure tsakanin ku, Aa ya saketa.

A wani zance kuma aka ce Auren ya warware kansa ba tare da anyi Saki ba. Kawai abinda yadace idan hakan ta faru toh ayi Saki a bata Takardan Sakin ta.
   Idan kafirai biyu suka Musulunta sai su ci gaba da zama a kan Auren, idan daya daga cikin ne ya Musulunta, toh wannan ya Warware auren su, ba tare da Saki ba, saidai idan itama zata Musulunta. Sannan idan kuma ita Matar ne ita ce ta Musulunta, toh shi ne ya fi cancantar ta, idan ya Musulunta kafin ta gama Idda, idan shi ya Musulunta Alhalin ita Matar Bakitabiya ce, toh sai ya ci gaba da rike ta a matsayin Matarsa, 
       Idan kuwa bamajusiya ce ta musulunta bayan Musuluntarsa ba tare da 'bata lokaci ba, toh sai su ci gaba da Auren su, idan kuwa an sami lokaci mai tsawo ne, toh ta yi masa Nisa kenan saidai ya Nemi wata. Idan Mushriki, ya Musulunta alhalin yanada Mata fiye da 4 tare da shi, toh sai ya zabi guda 4 daga cikin Matan nashi, sauran kuma ya rabu da su_____

Ku biyo mu a Fitowa na Gaba in Allah yakaimu.

Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.

Muhammad Tukur Jalingo
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Mana Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta Number WhatsApp Namu 
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.
Post a Comment (0)