SHAN AZUMIN MAI CIKI KO MAI GOYO


SHAN AZUMIN MAI CIKI DA MAI JEGO: RAMUWA KO CIYARWA?
Abu na farko da ya kamata a sani cewa, ba ya halasta ga mai ciki ko mai jego ta sha azumi don kawai tana da juna biyu ko tana shayar da jariri. Sai dai in akwai tsoron cewa azumi zai iya cutar da lafiyarta ko ya jawo mata matsala ita kanta ko danta ko kuma su duka biyun. Idan ya tabbata cewa in ta yi azumi akwai matsala, to a lokacin ne ya halasta ta sha azumi.
Malamai sun yi sabani game da hukuncin mace mai ciki ko mai jego in ta sha azumi, shin ramawa za ta yi ko ciyarwa ko kuma duka biyun? Akwai maganganu malamai kamar haka.
MAGANA TA FARKO
Abu Hanifah da Ibrahim Annakha’iy suna da ra’ayin cewa abin da ke kanta shine ramuwa kawai. Wannan kuma shine mazhabar Aliyu Dan Abu Dalib (Allah ya qara masa yarda)
MAGANA TA BIYU
In mace mai ciki ko mai shayarwa ta sha azumi saboda tana tsoron lafiyarta za ta rama ne kawai. In kuma ta sha ne saboda tsoron lafiyar danta da/ko abin da ke cikinta to za ta rama tare da ciyarwa. Wannan ita ce maganar Maliku da Sufyan da Shafi’iy da Ahmad Bn Hanbal. Hakanan kuma Al-Jassas ya hakaito irin wannan fatawa daga Abdullahi Dan Umar (Allah ya qara musu yarda) Haka nan ma Maliku ya hakaito a Muwadda daga Ibn Umar din.
MAGANA TA UKU
In mace mai ciki ko mai shayarwa ta sha azumi abin da ke kanta shine ciyarwa kawai, babu ramuwa. Ibn Abbas (Allah ya qara musu yarda) shine ke da wannan ra’ayin cikin sahabbai. Haka nan kuma Ibn Qudamah ya hakaito irin wannan magana daga Ibn Umar (Allah ya qara musu yarda).
MAGANA TA HUDU
Mai shayarwa in ta ji tsoro saboda jaririnta to za ta sha ruwa sai ta ciyar. Mai ciki kuma in ta sha za ta rama ne; domin ta fi kama da maras lafiya. Wannan shine mazhabin Alhasan Albasariy.
MAGANA TA BIYAR
Idan mai ciki ko mai jego ta sha azumi to ciyarwa ne akanta ba bu ramuwa, amma tana da zabin ta rama ba tare da ciyarwa ba. Wannan ita ce maganar Ishaq Dan Rahwuya.
Almubarakfuriy ya naqalto maganar Ibn Hajrin a inda yake cewa: “An yi sabani game da mai ciki da mai shayarwa da kuma wanda ya sha azumi saboda tsufa in ya sami qarshin ramawa daga baya. Shafi’iy ya ce: za su rama kuma su ciyar, Auza’iy da mutanen Kufa suka ce ramuwa ce kawai akan su banda ciyarwa”. Sa’annan ya ambaci maganganun malamai mabambamta sannan ya ce: “Abin da ya bayyana gare ni shine cewa mai ciki da mai shayarwa suna daukan hukuncin maras lafiya ne da matafiyi. Allah shine mafi sani”.
Haka nan Ibn Qudama ya hakaito maganganun malamai da hujjojin su akan mas’alar sannan ya tabbatar da cewa abin da yake ganin shine daidai shine ramuwa ce akan matar da ta ji tsoro don kan ta, da kuma ramuwa da ciyarwa a kan wacce ta ji tsoro saboda kan ta da kuma yaronta.
Ibn Bazz ya fadi cewa: “da mai ciki da mai shayarwa [in sun sha azumi] hukuncinsu shine irin hukuncin maras lafiya. Saboda haka in sun kasa yin azumi za su rama daga baya. Wasu malamai kuma sun tafi izuwa ga cewa ciyarwa za su yi, amma wannan magana ce mai rauni. Abin da yake daidai shine ramuwa ce akan su kamar yadda take kan maras lafiya da matafiyi idan sun sha azumi”. Sannan ya kara cewa: “abin da yake daidai shine mai ciki da mai jego in sun sha azumi su rama. Abin da aka ruwaito daga Ibn Abbas na cewa ciyarwa ce kawai a kansu wannan zance ne mai rauni kuma ya saba wa dalilai na shari’a…”.
A cikin fatawar majalisar qoli ta malaman kasar Saudia sun ce: “In mace mai ciki ko mai sharyarwa ta ji tsoron abin da zai faru gare ta ko ga dan ta sai ta sha azumi to ramuwa ne akan ta, hukuncin daya ne da hukuncin maras lafiya wanda ya kasa yin azumi saboda tsoron cutarwa ga kansa. Allah ya ce: (Kuma wanda daga cikinku ya kasace ba shi da lafiya ko kuma yana halin tafiya [in ya sha azumi] to ya rama adadin kwanakin da ya sha daga baya [Baqara, 185])”. Sannan suka sake cewa: “Ita kuwa mai ciki, ya wajaba akan ta tai azumi sai dai in ta ji tsoron cewa azumin zai cutar da ita ko ya cutar da abin da ke cikinta, to anan an yi mata rangwame ta sha azumi, sannan ta rama bayan ta haihu ta kuma kuma tsarkaka daga jinin biqi…. Kuma ta sani cewa ciyarwa ba za ta sauke mata nauyin azumin ba, lallai dole ne ta rama azumin da ta sha”.
Ibn Uthaymin ya ambaci zantukan malamai game da wannan mas’ala sannnan ya karkata izuwa ga cewa sai ta rama, sannan ya ce: “Wannan maganar a wajena it ace magana mafi rinjaye, saboda abin lura shine hukuncin mai ciki da mai shayarwa kamar hukuncin maras lafiya ne da na matafiyi”. 
A qarshe, abin da ya fi bayyana daga maganganun malamai game da wannan mas’ala shine riqo da asalin cewa: duk wanda ya sha azumi saboda wani uzuri da sha qarfinsa to ramuwa ce akansa. Ba za a tafi zuwa ga fatawar ciyarwa ba sai ga wanda ya kasance yana tare da ciwo ko larurar da ba a sa ran warkewarta.
Allah shine mafi sani.
Asgar2020
Post a Comment (0)