*TAMBAYA TA 304*
YAYATA ANNOBA:
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Muna roƙon malam ya yi mana nasiha game da surutu da yayata annoba, tun da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi hani da hakan. May be (me yiwuwa) in al’umma suka ga hadisi za su hankalta.
AMSA A304:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Was Salaatu Was Salaam Alaa Nabiyyinaa Muhammadin Wa Alihi Wa Sahbih.
(1) Idan ana nufin yayata annoba ta hanyar maganganu a kan ta - kamar yadda zahirin tambayar ta nuna - to, ni dai ban san wani hadisi sahihi da ya yi magana a kan haka ba. Sai dai a tambayi manyan malamai. Wal Laahu A’lam.
(2) Idan kuwa yayatawa yana nufin yawo da annobar ta hanyar tashi daga garin da ta auku zuwa garin da ba ta auku a cikinsa ba, wannan kam akwai riwayoyi ingantattu masu yawa da suka hana hakan, kamar maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
« إِنَّ هَذَا الْوَجَعَ أَوِ السَّقَمَ رِجْزٌ عُذِّبَ بِهِ بَعْضُ الأُمَمِ قَبْلَكُمْ ثُمَّ بَقِىَ بَعْدُ بِالأَرْضِ فَيَذْهَبُ الْمَرَّةَ وَيَأْتِى الأُخْرَى فَمَنْ سَمِعَ بِهِ بِأَرْضٍ فَلاَ يَقْدَمَنَّ عَلَيْهِ وَمَنْ وَقَعَ بِأَرْضٍ وَهُوَ بِهَا فَلاَ يُخْرِجَنَّهُ الْفِرَارُ مِنْهُ »
Haƙiƙa! Wannan cutar ko rashin lafiyan azaba ce da aka yi wa wasu al’ummoni a gabanin ku, sai kuma wani abu daga cikin ta ya saura a duniya. Shi ne yake tafiya wani lokaci, wani lokacin kuma ya komo. Don haka, duk wanda ya ji labarinsa a wata ƙasa, to kar ya shige ta, kuma wanda ciwon ya auku a ƙasar da ya ke cikinta, to kar guje mata (da jama’a ke yi) ya fitar da shi daga gare ta. (Sahih Al-Bukhaariy: 6974, Sahih Muslim: 5948).
Wannan lafazin Muslim kenan. A cikin lafazin riwayar Al-Bukhaariy kuma ya ce:
« وَمَنْ كَانَ بِأَرْضٍ وَقَعَ بِهَا فَلاَ يَخْرُجْ فِرَارًا مِنْهُ »
Wanda kuma ya ke cikin ƙasar da ta auku a cikinta, to kar ya fice yana mai guje mata.
Hikimar wannan hanin, in ji malamai shi ne: A kare sauran jama’a ta hanyar hana shi yaɗa cutar a wuraren da ba ta kai musu ba.
Allaah ya kyauta.
(3) Sannan musulmi ya sani, bin wannan dokar ba zai haifar masa da asara ba. Domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi magana a kan annoba, ya ce:
« أَنَّهُ عَذَابٌ يَبْعَثُهُ اللَّهُ عَلَى مَنْ يَشَاءُ ، وَأَنَّ اللَّهَ جَعَلَهُ رَحْمَةً لِلْمُؤْمِنِينَ ، لَيْسَ مِنْ أَحَدٍ يَقَعُ الطَّاعُونُ فَيَمْكُثُ فِى بَلَدِهِ صَابِرًا مُحْتَسِبًا ، يَعْلَمُ أَنَّهُ لاَ يُصِيبُهُ إِلاَّ مَا كَتَبَ اللَّهُ لَهُ ، إِلاَّ كَانَ لَهُ مِثْلُ أَجْرِ شَهِيدٍ »
Tabbas! Ita wata azaba ce da Allaah ke aika shi ga wanda ya ga dama. Kuma Allaah ya sanya ta Rahama ce ga muminai. Babu wanda annoba za ta auku sai shi kuma ya zauna a cikin garinsu, yana mai haƙuri, mai neman sakayya daga Allaah, yana sanin cewa, babu abin da zai shafe shi sai dai abin da Allaah ya ƙaddara masa kawai, face yana da misalin ladan mai mutuwar shahada. (Sahih Al-Bukhaariy: 3474).
Cewa: Ya zauna a garinsu… wannan bai hana shi bin dokokin da mahukunta suka kafa a wannan ƙasar da sauran ƙasashe da jihohi, na hana mutane fita daga cikin gidajensu ba, domin aiki da shawarwarin masana harkar likitanci da kiwon lafiya. Wannan ma mataki ne na hana yaɗuwar wannan cutar ta coronavirus a cikin al’umma.
(4) Dakatar da zuwa masallatan jam’in salloli a unguwanni da zuwa sallar Jumma’a a garuruwa, da ɗage halartan darussan Tafsiri da Sallolin Asham ko Taraawih a cikin masallatai, ga kuma dakatar da zuwa Umrah a cikin watan Azumin Ramadan, sannan wataƙila ma da dakatar da aikin Hajji na wannan shekarar, duk manufar su kenan su ma: A hana mutane cuɗanya ko cakuɗa da juna, gudun kar mai ɗauke da ƙwayoyin cutar ya shafa wa mai lafiyar da ba shi da ita, alhali wataƙila shi ma bai san yana ɗauke da su ba!
(5) Muhimmin abin da ke a kan kowane musulmi a cikinmu a waɗannan lokutan na azumi da hajji, musamman mawadata, shi ne: Su ɗebo kuɗaɗen da suka yi tattali domin zuwa Umrah ko Hajjin, su juyar da su ga wani abin da zai sama musu ladan da ya fi na zuwa Hajji ko Umra, in shaa’al Laah. Wannan abin kuwa shi ne: Su sayo kayan abinci da abin sha, su rarraba wa talakawa da marayu da marasa ƙarfi a cikin wannan azumin. Don samun kyakkyawar sakamako sai su fara da bin unguwanni da gidajen talakawan tun yanzu, su ɗauki sunaye magidantan da suka cancanya a ɓoye, daga baya kuma sai a bi su da kayayyakin kuma a tabbatar kowa ya samu, shi ma ɗin a ɓoye.
(6) Haka labarun da ake yadawa a cikin tashoshin internet na facebook da whatsapp da sauransu cewa, wannan matsalar ta coronavirus duk farfaganda ce kawai na wasu ’yan jari-hujja, masu son samun ƙazamar dukiya a ƙarƙashin tsohon shirinsu na rage yawan al’ummar duniya ta hanyar samar da allurar rigakafi, wannan ma ba zai hana bin waɗannan dokokin nan da gwamnati ta sa ba.
(7) Sannan duk da cewa masu maganar sun kafa dalilai da irin waɗannan hujjojin wai:
(i) In Jan. 2017, Dr. Anthony S. Fauci, a director in NIH, told a crowd in Georgetown University Medical Center that, there will be a surprise inevitable pandemic during Trump’s administration!
Tun a watan Janairun 2017 aka ji wani Dr. Anthony S. Fauci wanda ke aiki a wata ma’aikatar lafiya a Amirka mai alaƙa da Bill Gates yana faɗa wa wani taron jama’a cewa: Ba makawa a lokacin mulkin Trump za a samu ɓarkewar wata annoba mai ban-mamaki!
(ii) In Oct. 2019, Bill Gates funded Event 201 a simulation that estimated a total of 65 million people killed by coronavirus.
A watan Oktoba na 2019 wannan Bill Gates ya ɗauki nauyin wani taro: Event 201 wanda ya ƙiyasta cewa mutane miliyan sittin da biyar (65,000,000) za su mutu ta dalilin coronavirus!
(iii) in Nov. 2019, The Pirbright Institute funded by Bill Gates was issued with European Patent Specification no. EP3 172 319 B1 to produce coronavirus vaccines to treat humans.
A watan Nuwamba na 2019 ɗin dai aka ba wata cibiyar da Bill Gates ke ɗaukar nauyin ta: The Pirbright Institute takardar izini mai lamba: European Patent Specification no. EP3 172 319 B1 don samar da allurar rigakafin cutar coronavirus!
(iv) Anthony Fauci says: Coronavirus might keep coming back year after year, and the ultimate game changer in this will be a new vaccine.
An ji wancan Dr Anthony Fauci ɗin dai yana cewa: Cutar coronavirus za ta cigaba da maimaituwa shekara-bayan-shekara, kuma a ƙarshe abin da zai sauya tsarin kawai shi ne: Samun sabon allurar rigakafi!
(v) Bill Gates is saying: Mass gatherings might not return until we get coronavirus vaccine!
Sannan shi kansa Bill Gates an ji shi yana ambaton cewa: Taron jama’a a wuri guda ba zai komo a cikin al’umma ba, har sai mun samu allurar rigakafin coronavirus!
(vii) In Australia the President told his people that the only way for them to get out of their homes is to accept vaccine!
A ƙasar Australia kuma wai an ji shugaban ƙasar yana faɗin cewa: Hanya ɗaya da mutane za su iya samun daman fita daga cikin gidajensu ita ce ta amincewa da allurar rigakafi!
Waɗannan maganganun duk ba za su hana mutane ɗaukar irin waɗancan matakan da Hukuma ta tsara na kariya daga cutar ba.
(8) Amma dai su shugabanni da jami’an tsaro ne ya kamata su san hakan, kuma su binciki waɗannan labaran don tabbatar da sahihancinsu, musamman dayake a ƙa’ida ba a yin sakaci da kowane gutsuren labara da ya shafi tsaron rayuwa da lafiyar al’umma.
Lallai a binciki irin waɗannan bayanan tun da wuri kafin wani mahandami ya shigar da ra’ayin fara zarƙama wa jama’a sinadaran da za su janyo musu hallaka da sunan allurar rigakafin cutar coronavirus (covid-19).
Allaah ya kiyaye.
(9) Muna roƙon Allaan Maɗaukakin Sarki, Mabuwayi Mai Girma ya kare Gwamnatocin ƙasashenmu, ya ba su tarin hikima da basira har su iya kauce wa duk abin da zai zama cutarwa ga al’umma, ya sa su iya janyo mana duk abin da ke zama alheri ga al’ummar ƙasa baki-ɗaya. Kuma Allaah ya shiga tsakaninsu da duk waɗanda suke shirya maƙarƙashiya domin cutar da ƙasa da jama’ar ƙasa a kusa ko a nesa.
(10) Ya Allaah! Ya Ubangijinmu! Ka gafarta wa duk musulmin da suka rasu ta dalilin wannan cutar, ka yafe musu, kuma ka karɓe su a matsayin shuhada’u a duk inda su ke. Waɗanda suke fama da cutar kuma, Allaah ka warkar da su a ko’ina su ke. Sauran jama’a kuma, ka kare mu daga kamuwa da ita da sauran ƙanana da munanan cututtuka a duk inda mu ke a sassan duniya, don Girman Ikonka da Buwayarka.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
17/4/2020
2: 53pm.
Majlisin sunnah
08164363661
