MU'AMILLA DA CORONA.
1
Kamar yarda masana kiwon lafiya da hukumomi da shuwagabanni suka tabbatar da Annobar CORONA Gaskiya ce, tana wanzuwa a doron Duniya a halin da ake ciki. Haka zalika na san babu mai tantama akan rayuwa da hanyoyin inganta rayuwar suma wajibi ne ga wadanda suka kasance a Raye a Duniyarmu a yau.
Abin nufina anan shine: Wadanda suka kasance a raye ya wajaba su ci su sha su yi addini, idan ba su da lafiya su sha magani. alal-akalla an sami jigogin a rayu a doron duniya idan wadannan suka samu.
Idan muka yi la'akari da kasashen da suka cigaba a Duniya muna da banbanci da su tin daga tsarin gidajen kwana. ina nufin hukumominsu na tsara birane da karkara suna aiki ba zaka dasa Tirgadar gina muhallin kwanciya ba sai da sanin Hukuma kuma akan doron dokar hukuma. wannan ta bada damar saukin kididdigar gidaje da mamallaka gidajen sabanin irin gidajenmu masu kama da SHURI.
A hirar da muka yi da Dw.hausa a satin da ya wuce wani mazaunin Saudiyya da ba dan kasar ba ya shigo ya bayyana yarda Hukuma take tallafawa duk mabukacin da ya bukaci abin masarufi har gida. ta hanyar Wayar salula zai kira ya zabi abinda ya ke so na daga abinci ya zayyana adadi a kawo masa har gida. Gaya min ta yarda hukuma zata ce zauna a gida ya ce sai ya fita?
Mahukuntanmu sun nuna ba za su iya ciyar da mu ba gabakidaya ga shi kuma cin abinci dole ne, sun gwada ba za su iya kula da lafiyarmu ba har an kulle asibitoci marasa lafiya basa ganin likitoci saboda Annoba. Ga shi kuma kula da lafiya ya zama dole har ma marasa lafiyar cikinmu suna ta rasa rayuwakansu a sakamakon rashin ganin likitoci.
To abin tambaya anan shi ne: Me ya sa muka dauki tsarin wadanda suka fi mu arziki da cigaba muka kakabawa Al'umarmu alhalin mun san ba zamu iya ba? Me ya sa ba zamu nemi masana su samar da shawarar MU'AMILLA A HALIN RAYUWA DA CORONA BA?
Ita corona sai ta rayu zuwa wa'adin da aka deba mata, haka muma sai mun rayu zuwa wa'adin da Allah ya deba mana a rayuwarmu a duniya. To sai mu kakaba takunkuminmu da ma safar hannu har ma da ta kafa kowa ya saka Abin wanke hannu a aljihunsa da cikin Kaja mu koma aiki tare da bada tazarar Taki biyu da kan fada, kada tattalin arzikinmu ya ida Kurmushewa kurmus! Dama kuma kowa ya san babu shi tinda ba za a iya ciyar da yan kasa su zauna a gida ba kamar yarda tsarin yake nunawa.
Amma ku ya kuke gani a naku hange ta yaya zamu rayu a cikin wannan Karni na Annobar CORONA?
