*FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN*
=
=
*DAGA ZAURAN*
=
*TARBIYYATUL AULAD*
=
*What'sApp*
```08168315013```
```08162332323```
=
*=15/9/1441*
*8/5/2020*
*FITOWA TA TALATIN*
.Cigaban Karatun littafin
_FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN_ _Akan koyarwar Alqur'ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na kwarai._
*LITTAFI NA DAYA*
*NA*
```SHEIKH ABDULWAHAB ABDALLAH```
=
=
*TAMBAYA TA 49*
```Mutum ne yace ko ya sha ku ya kusance iyalin sa bisa tsammanin rana ta fadi ko alfijir bai keto ba, mene ne hukuncin sa```
*AMSA :*
Manyan malamai sunyi sabani akan wannan. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa zai yi ramuwa, ba tare da kaffara ba, wasu kuma daga cikin manyan malamai magaba ta kamar su Ibn Rahawaihi da Imamu Ahmad da Ibn Taimiyyah suna ganin cewa wanda hakan ta faru akansa, ba zaiyi ramuwa ba. Dalilin su kuwa shine hadisin Adiyyi Ibn Hatim yayin da Allah ya saukar da ayar:
*وكلوآ واشربواحتى يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر*
Ma'ana:
...ku ci ku sha har yayin da farin zare ya bayyana daga baki na alfijr.
Adiyyu Allah ya qara masa yarda yace sai na ajiye zare baki da fari a karkashin matashin kaina, nayi ta cin abinci ina dubawa har sai da gari ya waye.Amma da Adiyyu Allah ya qara masa yarda ya gaya wa Manzon Allah tsirada amincin Allah suqara tabbata agareshi bai ci masa ya rama azumi ba. Wannan shine zance mafi rinjaye a wajenmu ,saboda Adiyyu Allah ya qara masa yarda yayi wannan ne bisa kuskure ku jahilai. Haka shima wanda ya ci ko ya sha ko ya kusanci iyalinsa bisa tsammanin rana ta fadi ko alfijir bai keto ba,shi ma yayi hakanne bisa kuskure ko jahilci.
_Zamu dakata anan sai lokaci na gaba da yardar Allah_
=
=
✍🏻. *RUBUTAWA*
```RUQAYYA AUWAL USMAN```
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka Wanatubu ilaika
