TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 13


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//13📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Irin wannan adalci da muke magana a kai shi ne babban dalin da zai sa fandararren mutum ya karbi gaskiya, sai ya fado wasu dalilai dake sanya mutane su gaza yi wa sauran adalci, ya ce "Ka sani, dalilan dake hana mutum ya yi nesa da adalci ya abka cikin son kai suna da yawa [Ya zayyano su]:-

1) Mutum ya raya a wani wuri wanda mutanen wurin suna kan wata mazhaba ta masamman, inda za su yi karatu a wurin wani malami, wannan mazhabar kadai zai nuna musu ba zai ambato daidai din wata a kan tasa ba.

2) Ga son girma na jagoranci da son dukiya, samun da damar kai-komo wurin manya da sarakuna, a qarshe a dan nemi abin hannunsu, duk lokacin da zai fidda wani hukunci to zai yi daidai ne da abinda suke so ba zai yi adalci ba.

3) Jayayya da tauna-tauna da wasu daliban ilimi ko malamansu suke yi, wanda a qarshe ya kai ga an fito munazara, sai son a san mutum ya bayyana da son rinjaye a kan wasu, daganan duk abinda zai qarfafa shi kawai zai rarumo ba zai yi adalci ba.

(Wannan gaskiya ne, na ji tattaunawar da wani ya kafe wai ba a karanta daidai ba, ya ce an saba wa hukuncin nahawu, wani kuma wai an yi kuskure a shafin littafin da ya fadi, ko kuskuren fadin sunan, shikenan ya zama dalilin da ba za a karbi hujjarsa ba, wani kuma wai bai iya Larabci ba, akwai wanda aka tsaya sai ya fado makarantar da ya yi, ya fadi kwalinsa kafin a ci gaba da tattaunawar, duk wadannan in ka duba ba su da alaqa da ainihin batun da ake son a tattauna, in an gaza yin adalci a kan wannan ban san abinda za a yi adalcin a kai ba).

4) Mutum ya koma zuwa ga makusantansa kamar malaman da ya yi karatu a wurinsu ya kalato duk wata hujja da za ta qarfafa shi, abin kula dai shi ne yin amfani sunan wadannan malaman da kowa ya san su, sai ka ga ya karkata koda kuwa su ma kuskure suka yi a mas'alar, ba zai yi adalci ba.

5) In mutum ya yi wata fatawa daga baya ya gano kuskurenta ya canja, kuma wannan barnar ta shahara kowa ya san ta, sai a dage kanta a matsa masa da ita ba za a yi adalci ba don dai a kare wani ra'ayi.

6) Ko in mutum ya ga cewa wanda yake tauna-taunannan da shi fa yaro ne, ko kuma bai ma kai shi ilimi ba, sai ya ji tsoron qasqanci ko gocewar shuhura sai ya dage a kan ra'ayinsa ya qi yin adalci wurin karbar gaskiya.

7) Mutum ya tsaya a kan wasu qa'idoji wadanda zai amince da duk abinda ya yi daidai da su, ya qi karbar abinda zai saba musu, bayan kuma ba wanda zai ce su ma din ba za su iya zama kuskure ba, da haka sai ya to yin adalci.

8) Komawa littafan fiqihu na mazhaba don samun dalilin da zai qarfafa shi a kore wani dalilin da mai tauna-taunar da shi zai kawo, ko ya yake kuwa matuqar ya saba wa mazhabar da yake kai.

9) Tsayawa a littafan dake tankade da rairaiya kan malamai, wadanda masu wadannan fahimtar suka rubuta, bayan kuwa masu duba irin wannan littafan a yau kan karbi wanda ya yi musu ne su wanke wanda ya saba musu su yi masa tas.

10) Gasa a tsakanin malamai wadanda kusan matsayinsu ko matakinsu na ilimi yake kusa da kusa, wanda hakan zai iya sakawa wani ya kuskuranta daya ba tare da tabbacin ya yi kuskuren ba, dondai kawai ya kare fahimtarsa.

11) Dagewa kan wasu ra'ayoyi ko zantukan malamai a kan wani fanni na ilimi dake ginuwa a kan fahimta da ta cakudu da ijtihadi, kamar dai Usulul fiqhi, sai mutum ya sami wata qa'ida ya dafe mata ya qi yin adalci (Adabut tibb 31/121).

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa:Abulfawzhaan*
Post a Comment (0)