IDAN BAKA YABA MATA BA TO KADA KA KUSHE MATA.
Ya kai dan uwa albarka kada ka kasance mai rashin yabawa iyalanka, ko iyayenka akan abunda suka dafa maka na buda baki, ka kasance mai yaba musu, mai jinjina musu da kuma yimusu addu'a ta alkhairi akan bajintar da sukayi na dafa maka abunda zakayi buda baki dashi.
Kasani bayin Allah nan suna kokari matuka, lokacin dafa abun buda baki shine lokacin da duk wani mai azumi ya galabaita, ya jikkata su kuma awannan lokacin zasu daura haraman shiga kitchen domin sama maka abunda zaka samu kayi buda baki dashi, batare da kuma kosawa ko gajiyawa ba. Butulcine kushe musu abisa wannan kokari da suke.
Ka yaba musu, ka kuma godemusu Sannan ka kuma musu addu'at Alkhairi.
Ya Allah ka kara albarka ga iyayenmu mata, da matanmu, kannenmu yayunmu, da duk wata da take kai komo wajen ganin ta samawa jama'arta abun buda baki.
#zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
