KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA JUGOL BIU BORNO STATE 🌐 30/SHAWWAL/1442-HJRY 🌐 11/JUNE/2021-MLDY


KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA JUGOL BIU BORNO STATE
🌐 30/SHAWWAL/1442-HJRY
🌐 11/JUNE/2021-MLDY

🎙️ *GABATARWA👉🏼 Abubakar BN Mustafa Biu*

⭕ *TOPIC👉🏼 [MAI SAƁAWA IYAYE- ƊAUKI DARASI DAGA ƘISSOSINNAN GUDA 4]*

➖ _MUN KASASHI GIDA 5️⃣_

1️⃣👉🏼 *ƘISSA TA FARKO*
  Wani Matashine mai suna *MANAZIL* shi mutumin banzane mai saɓawa mahaifinsa, Mahaifinnasa Mutumne mai addini amma aduk lokacinda yakira yaron yayi masa nasihar cewa yadaina biyewa giggiwar kuruciya da iskancinta dominfa *ALLAH SW* mai ɗaukan fansane, sai yaron yayi biris yadaɗa zurfafawa cikin kangara, Rannan Dattijon yana masa nasiha yadda yasaba sai yaron yaɗaga hannu yabugi dattijonnasa😢, cikin kuka dattijonnan yasha alwashin zuwa *ka'aba🕋* yariƙe rigarta yayiwa yaron mugun adu'a akan hannunda yabugeshi dashin yashanye, hakan kuma yayi nan take rabin jikin yaron yashanye, dubi littafin
  *عقوق الوالدين- للشيخ علي القرني* 
 *DARASI=* girman munin cutarda iyaye/ gaggautuwar faɗowar masifa akan mai cutarda iyayensa

2️⃣👉🏼 *ƘISSA TA BIYU*
  Matashine a wannan zamanin yasha yunƙurin watsarda tumakin babansa dayake kiwo don yabi matasa zuwa neman aikin soja, amma babansa yaƙi bashi izinin yatafi don bashida mai kulawa da dabbobinnasa, rannan yaron yacewa babannasa= ko kabani izini ko baka baniba zan tafi neman aikin sojan, Babannasa yace= ƙarfi kam bani dashi ammafa inada kibiya🏹 mai ƙarfi dazan nema awurin *ALLAH* wato adu'a, Yaro yanemi guzurin tafiya wurin wata cikin danginsa yakama hanya yatafi, Da baban yaga haka sai yaɗaga hannu👏🏻 dafda asuba yace= ya *ALLAH* kanunawa yaronnan abin ƙi, nan take yaronnan yamakance a hanyarsa ta tafiya, sai wasu 'yan garinsu sukace dashi yanzu ya za'ayi⁉️ Sai yace= kudawo dani gida kawai don baza'a ɗauki makaho sojaba, haka suka iso dashi gida cikin dare, sai babansa yace= kibiyar tawan ta samekane⁉️ Yaron yace= ƙwarai kuwa baba yasameni a ido na makance, cikin tausayi da alhini babannasa yace= ai bansan a ido zai samekaba, nan take yafara ƙiyamullaili a wannan daren yanata roƙon *ALLAH* yadawowa ɗan nasa da idanunsa, kafin asuba idanun yaron suka dawo🙂, SHEYKH ALIY ALQARNY yace= yawancinmu anan mun san yaron da mahaifinnasa, dubi littafin
 *عقوق الوالدين- للشيخ علي القرني*
 *DARASI=* Mai saɓawa iyaye baya dacewa aduk abinda sukasa agaba/ adu'ar iyaye ga 'ya'yansu abin karɓane cikin gaggawa na alhairi ko sharri/ ashe iyaye na iya janye tsinuwarsu akan 'ya'yansu kuma yajanyu

3️⃣👉🏼 *ƘISSA TA UKU*
  *ABAN IBN IYASH* yace= nafito bayan azahar daga gidanda *ANAS IBN MALIK R/A* yakeda zama abakin kasuwa lokacinda yakeda zama a *BASRAH* sai naga an wuce da gawa amma mutane 4 ne kacal ke rakata jana'iza, cikin kaɗuwa nace= *SUBHANALLAH* musulmi guda amma ace mutum 4 ne kacal zasuje masa jana'iza? don samun wannan amsan nabisu aka bizne dani, sai na tambayesu= meye sha'anin gawannan⁉️ sai suka nuna wata mace atsaye awaje da maƙabartar sukace- mumafa wancan matarce taɗau leburancinmu tabiyamu don muzo muyi jana'izar,
  *ABAN* yace= sai nabiyota zuwa gida na mata ta'aziyyarl kuma na mata tanbayar, sai tace= Wannan yaronane mai aikata aikin saɓo ƙwarai kuma mai matuƙar saɓa mini, yayinda ajali yazo masa yaroƙeni yace= ya mamata, kiriƙa mini talƙini kuma idan namutu muddin kinason in kuɓuta daga azaba- to kisa dunduniyar ƙafarki a kumatuna kice= wannan shine sakamakon mai saɓawa *ALLAH* kuma kada kisanarda kowa mutuwata domin babu mai halartar jana'izata saboda miyagun halayyata, kawai kinemi leburori 4 dazasu bizneni, ana bizneni muddin kinason in rabauta kiɗaga hannu sama kice= *ya ALLAH! na yafewa ɗana kuma nayarda dashi- kaima kayarda dashi👏🏻* tace= hakan kuma nayi,
  *ABAN* yace= sai naga matar tayi murmushi🙂 tace= bayan an bizneshi nayi wannan sai naji muryarsa yana cewa= *mama! na gabato zuwaga UBANGIJI mai karimci da jinƙai kuma baiyi fushi akainaba*
 *ALLAHU AKBAR! babu adu'arda takai na iyaye! babu waɗanda muke buƙatar adu'arsu da yardarsu bayan yardan ALLAH SW sai iyaye* dubi littafin
 *عقوق الوالدين- للشيخ علي القرني*
 *DARASI=* ƙarfin adu'ar iyaye/ yardan iyaye shine yardan *ALLAH SW* ne hakama fusatar dasu fusatarda *ALLAH SW* ne

4️⃣👉🏼 *ƘISSA TA HUƊU*
  Wani Matashine mai saɓawa iyaye yaɗauko mahaifinsa yazo dashi daji ya ajiyeshi a ƙarƙashin dutse yace= zan yankaka! Sai mahaifinsa yanemi dalilin haka, sai yaron yace= ka tsufa kana gajiyar dani da ɗawainiyoyi da, sai baban yace= *indai sai ka yankani to kaini ƙarƙashin wancan dutsen gefen can domin nima acan nayanka mahaifina- kuma kaima kajira naka wallahi kaima ɗanka sai yazo ya yankaka anan muddin kayi hakan!* dubi littafin
 *عقوق الوالدين- للشيخ علي القرني* 
 *DARASI=* yadda kayi haka za'a maka/ mugun aiki yanada sakayya irinsa/ saɓawa iyaye bashine jikoki zasu biyawa kakansu

5️⃣👉🏼 *RUFEWA*
  Yaku bayin *ALLAH* munji abinda mukaji, don haka kowa yakalli kansa yaya yake mu'amalantar iyayensa⁉️sunefa madubin rayuwarka da makomarka! yadda ka mu'amalancesu hakama naka 'ya'yan zasu mu'amalanceka! inka kyautata kaima su kyautatama, in kuma ka munana musu- ka saɓa musu- ka kashesu da bindiga ko wuƙa ko guba ko tsafi ko ɓacin rai kasasu har hawan jini ko bugun zuciya yakarsu- *TO WALLAHI KAIMA KAJIRA NAKA‼️*
👏🏻 *YA ALLAH- KASA MUWANYE LAFIYA👏🏻*
 *AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻*

 *via*👉🏼 *Abubakar BN Mustafa Biu✍️*
Post a Comment (0)