HUKUNCIN KARBAR LOAN



HUKUNCIN KARBAR LOAN

                            *TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum, Malam menene hukunchin karbar bashi amma na kaya ma'ana kamar (Car loan,) ko nau'insu kamar abinchi, wanda mutum zai amsa ya biya zuwa wani lokaci, amma kuma farashin yana bambamta da wanda zai je kasuwa ya bayar da kudinsa ya siya. Shin akwai RIBA a cikin irin wannan loan din? Koko babu. Allah ya saka da alkhairi.

                                   *AMSA*👇

Wa'alaikum assalam, To dan'uwa Matukar an bayyana masa kudin tun da farko, to ba riba ba ne ko da ya sabawa farashin kasuwa, domin lokaci yakan yi tasiri wajan ciniki, saboda in har an biya 'yan kasuwa kudin su cikin lokaci to za su iya amfana da su, wajan sayo wasu kayan da za su ci riba, don haka malamai suka yi bayyani cewa hakan ya halatta, idan har an yi sharadi da farko.

Saidai abin da sharia ta hana shi ne : ayi kari akan sharadin farko, kamar ya sayar masa da abu naira (10,0000) sai ya zama ya kasa biya a lokacin da suka yi alkawari, sai ya kara masa 3,000 akai, wannan shi ne abin da ya haramta , saboda Annabi S.A.W ya hana yin ciniki biyu cikin ciniki daya. kamar yadda ya zo a hadisin da Malik ya rawaito a Muwada'a a lamba ta: 2640

Don neman Karin bayani duba: Fiqhul muyassar: shafi na: 219.

Allah ne mafi sani 

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

_Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana._ 

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)