WADANDA AKE BAWA ZAKKA !

WADANDA AKE BAWA ZAKKA !


*Tambaya*
Assalamu Alaikum, Dan Allah ina da tambaya ita zakka akwai wanda Allah ya lissafa aba, ko ko kai za kaba wanda ka ga dama ? nagode malam

*Amsa*
Waalaikumussalam 
Akwai su Mana, a cikin suratu Attaubah, Allah ya yi umarni a bawa nau'ukan mutane takwas :
1. Fakirai.
2. Miskinai.
3. Wadanda ake fatan jawo zuciyarsu zuwa Musulunci
4. Bayin da aka dorawa fansa, suke neman yadda za su biya.
5. Wadanda ake bi bashi.
6. Wadanda suke raba Zakka.
7. Dan tafarki Wanda kudinsa suka Kare.
8. Wanda yake aikin daukaka kalmar Àllah.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

28/10/2020

Zaku iya Bibiyar mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)