SHIN AKWAI GADO GA MATAR DA MIJINTA YA MUTU BATA GAMA IDDA BA?
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Malam mutum ne ya saki matarsa Bai dawo da ita ba kuma bata gama idda ba sai ya rasu, shin zata ci gadonsa?.
Allah ya kara ma mal imani DA ilimi mai amfani Ameen.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salaam Wa rahmatullahi wa barakaatuhu,
To dan'uwa Idan miji ya saki matarsa , kuma ya mutu kafin ta gama idda, to za ta ci gadonsa Mutukar saki ɗaya ne ko biyu, saboda har a lokaçın tana nan a matarsa, amma in uku ne babu gado a tsakaninsu, haka nan idan fansar kanta ta yi, saboda ta nisanta daga gare shi.
Allah ne mafi Sani.
Dr Jamilu Zarewa
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ