BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA (WANDA BA YA KISHIN IYALINSA)

BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA (WANDA BA YA KISHIN IYALINSA)
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum mallam da fatan mun tashi lafiya, malam tambayata ita ce wata ce tana da aure se take shiga facebook da WhatsApp tana gaisawa da maza suna charting wani lokaci ma suna kiranta a waya su gaisa, to wasu kuma abokanin huldar kasuwancinta ne, to ya halatta ta cigaba da gaisawa da su a addinance?
Amma ita da yerdar mijinta take shiga social media.

:
*AMSA*👇
:
Wa’alaikumus Salamu wa Rahmatullah, ƴar uwa kuskure ne babba a ce miji ya bar matarsa tana yin Facebook ko WatsApp da wasu maza wai da sunan abokannin kasuwancinta ne, saboda qara lalacewa ma har kiranta suke a waya suna gaisawa kuma duk mijin ya san da haka amma bai jin komai a ransa, to wannan ba dai-dai ba ne, kuma bai halasta ta cigaba da gaisawa da su a addinance ba.

Duk wata hulɗa da za ta iya sa mace da namiji su keɓanta ba tare da muharraminta ba bai halasta ba ko da kuwa hulɗar addini ce kamar yadda aka bayyana a amsar tambaya ta 56, dalili a kan haka shi ne hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas, A inda Annabi ﷺ ya ce:  "Kada wani mutum ya keɓanta da wata mace face sai da muharraminta". Bukhariy 4955.

Saboda haka duk matayen da suke yin fira da mazajen da ba nasu ba a kafofin sadarwa na zamani da wajensa su ji tsoron Allah su daina, idan kuma ba za su daina ba su sani cewa Allah na sane da duk abin da suke yi, ba su isa su ɓoye masa komai ba.

Sannan kuma duk namijin da ke barin matarsa tana mu'amala da duk wanda ta ga dama, kuma ba ya damuwa da duk wanda suke shiga wurinta, to irin wannan miji shi ne mai tabbatar da ɓarna a cikin iyalansa, kuma Annabi ﷺ ya lissafa shi a cikin mutanen da Allah ya haramta masu shiga Aljanna, kamar yadda Abdullahi ɗan Umar ya ruwaito.
Musnadu Ahmad 5372.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)