HUKUNCIN JININ BARI.
Tambaya
Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Dan Allah idan mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin ya zaka na ciwo ko zata daina azumi sallah
Amsa
To dan'uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa: duk cikin da ya zube kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne daga 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka duk cikin da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za'a bar sallah da azumi.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.