_*======BUDURCI NA=====*_
*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*
*Fitowa ta daya=*{16}*
Wani bincike da hukumar gidan Radion BBC Hausa suka gudar wanda yakai su har kasar India sukaci gaba cewa,
Kungiyar wasu matasa a wani gari da ke jihar Maharashtra a yammacin kasar Indiya ta shiga fafutukar kawo karshen wata al'ada ta tilasta wa sabbin amare tabbatar da budurcinsu,
a lokacin da suka tare a dakin miji.
Kamar yadda Marath Prajakta Dhulap
ta rubuta
Anita mai shekara 22 ta ce irin takaicin da ta shiga a lokcin aurenta kan wannan al'ada, shekara biyu da ta wuce,
har yanzu idan ta tuna ba abin da take yi sai kuka kawai.
Kamar sauran takwarorinta mata a garinsu na Kanjarbhat, mai mutane kusan 200,000 wadanda yawanci suke a jihar Maharashtra,
an tilasta wa Anita yin wannan al'ada ta tantance budurci a ranar daurin aurenta domin a tabbatar da mutuncinta na nan ko ta riga ta san namiji a waje ko kuma ba ta sani ba.
Wannan al'ada ta zama wani daga cikin muhimman shika-shikan aure a cikin wannan al'umma,
inda majalisar magabatan garin mai matukar iko ke tilasta wa amaren yin wannan gwaji.
Yadda ake wannan gwaji ko al'ada shi ne, za a ba wa ango da amaryar da za a yi wa auren farin zanin gado,
sanna a je a kama musu daki a otal , wanda majalisar magabatan za ta biya ko kuma dangin amarya ko ango.
Ango da amaryar za su yi kwanciyarsu ta aure a wannan lokaci yayin da dangin amaryar da angon suke jira a waje.
Idan amaryar tayi jini a lokacin saduwar,
to shi ke nan ta tabbata budurwa, amma idan ba ta yi jini ba to za a dauki tsattsauran mataki a kanta.
Ango yana da damar ya fasa auren,
wato ya saki amaryar tasa idan a wannan kwanciya ta farko ba ta yi jini ba, sannan ita kuma amaryar sai a kunyata ta a bainar jama'a,
har ma danginta su yi mata duka,
saboda abin kunyar da ta jawo musu.
Wadannan mutane suna ci gaba da gudanar da wannan al'ada duk da bayanin da masana ke yi na karyata maganar cewa ba dole ne mace ta yi jini a saduwarta ta farko da namijiba.
Muhadu agaba insha Allah,
*GABATARWA Miftahul ilmi*
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248