IDAN MANIYYI YA TABA KAYA DOLE NE SAI AN WANKE SHI GABA DAYA?

IDAN MANIYI YA TA6A KAYA DOLENE, SE AN WANKESHI GABA DAYA ??
:
Daga zauren
Khulafa'ur-rashiidun
:
Assalama alaikum
inada tambaya meye hukuncin mutumin da yakwanta barci yafarka, yajike da maniyi? Kuma galokacin sallar asuba  ta kawo kai, shi kuma baida kayanda zai chanja, yayi sallah da su Iya najikinsa kawai?
:
                     ******
:
Wa alaikumussalam
   Na'am ba sharadi bane dan mutum yayi mafarki yajiqa jikinsa da maniyi, ace bazaiyi sallah da wannan kayan ba !!
  Abinda ya tabbata shine *zaka wanke gurinda ruwan maniyin ya ta6a, ko ka kankare idan ya bushe* kaman yadda hadisai sukayi bayani. Bukhari 229 muslim 289 daga Nana Aisha uwar muminai ALLAH yaqara mata yadda  tace "ina wanke janaba daga Tufafin Annabi Sallallahu alaihi wa sallam, seya tafi zuwaga sallah, kuma da sauran ruwan (wankin) ajikin kayan sa".
.
Aruwayar muslim " haqiqa na kasance ina kankare (janaba) ajikin tufafin annabi Sallallahu alaihi wa sallam, kankarewa, seyayi sallah dashi (kayan). (Hadisi na 38 a umdatul ahkam)
.
  Abin nufi in maniyyi ya bushe, se akan kare gurin, iyaka kankara me kyau!!
    ALLAHU a,alam
=
➡Muhammad Auwal Hussain Abu ja'afar
========================
*```Date* ```[29-07-1439]Hj {15-04-2018}
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2347035269582
+2348063796175
+2349033206238
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*

Post a Comment (0)