YA HALATTA NA AURI 'YAR MATATA WACCE BA NINE UBAN TA BA?

YA HALATTA NA AURI, YAR MATA TA WACCE BANINE UBANTABA ! BAYAN RABUWA NA DA MAHAIFIYAR TA !!!!
:
Daga zauren
Khulafa'ur-rashiidun
:
Asslam'Alaykum
malam barka da warhaka  ya aiki ya hkuri ya karatu don ALLAH malam wata tambayace mukeda kamar haka.malam mutum ne ya'auri mace bazaura wacce tama tsofemashi saikuma allaah yakawo rabuwarsu suka rabu amma basu haihu ba.amma ita tanada wata 'ya budurwa wacce tahaifa da tsohon mijinta
toh malam yanxu sunrabu da wan nan mijin nata kuma yaga 'yar ta yace yanaso kuma ita tace zata bashi amma ayi bincike wajen malamn sunnah aji ko'akwai aure tsakaninsu..shine nace subari a tambayeka malam mungode.
:
                        ******
:
Wa,alaikumussalam. Ekon ALLAH ai wannan ba aure a tsakaninsu, gashi har ya kusance ta, hakan yasa koda kuwa sukade suka rage a duniya, ba'a aure sedai su jira  mutuwa !
.
Domin ALLAH ya riga ya hana haka a suratun nisa'e, ga lissafin wadanda aka haramta Auran su⤵
(( An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mata, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku Nono, da 'yan'uwanku mãtã na shan nono, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi jima'e da su, kuma idan ba ku yi jima'ie da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, ALLAH Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.)) nisa'e 23
.
Idan bakada hali, ga wani za6in daga ALLAH.
(( Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma ALLAH ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma ALLAH Mai gãfara ne Mai jin ƙai.)) suratul nisa'e 25
   ALLAH ne mafi sani
=
➡ Muhammad Auwal Hussain Abu ja'afar
========================
*```Date* ```[29-07-1439]Hj {15-04-2018}
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2347035269582
+2348063796175
+2349033206238
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*

Post a Comment (0)