BAFFANA YANA YAWAN RAZANA A BACCIN SA

*_BAFFANA YANA YAWAN RAZANA A BACCINSA, A TAIMAKA MANA!!!_*

                                *Tambaya*
Assalamu alaykum: Mallam ina bukatan shawara ko mafita in Allah yasa kanada masaniya akai.

Uncle dinane ya kasance yakan yi mafarki da dare sai yake razana wani lokaci ya tashi da gudu ko yake kai duka, hakan wlh har yasa yakan ji ciwo sosai.

Kuma ya kanyi addu'o'i kamar karanta Kulhuwa, falaqi, Nasi, da ayatul qursiyu amma kuma abun yakan dame shi. Mafarkin nawani kamar macijine kebinsa.

Allah saka da alkhairi ya kuma sa mu samu mafita daga gareku ameen.

                                      *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Duk lokaçın da ya yi mafarki ya razana ya dinga karanta addu'ar da ta tabbata daga Annabi s.a.w. a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 3528.

أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه وشر عباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون

In har ya yi tofi sau uku a hagunsa ya canza bangaren kwanciyarsa, ba abin da zai cutar da shi, bayan haka.                 

Allah ne mafi sani.

11/04/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)