*_IDAN MAKUSANTA BIYU SUKA MUTU TARE, ZA SU GAJI JUNANSU??_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum.
Malam wani uba da danshi suka rasu alokaci daya kuma shi uban mai kudi ne.dan kuma ya rasu ya bar matar shi da ciki kuma bai bar komai ba. To Malam tambayata anan yaya zaa raba gado? Shin zaa rabu dukiyar baban ne da ya rasu tare da dan sai a ba matarshi da abinda ke cikinta ka sonshi koko shi dan tunda tare ya rasu da baban bashi da gadon dukiyar shi??
*Amsa*
Wa'alaikum assalam. Idan Makusanta biyu suka mutu tare, ba'a San Wanda ya riga mutuwa ba, to babu gado a tsakaninsu a zance mafi inganci, saboda yana daga cikin sharudan gado tabbatar da mutuwar Wanda Za'a gada Kafin Wanda zai yi gado, nan kuma ba'a samu tabbacin ba, don haka ba za su gaji juna ba, saidai kowa wasu magadan na shi na daban su gaje shi.
Allah ne mafi sani
14/04/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.