HUKUNCIN MAI KOMA WA CIKIN ZUNUBI BAYAN YA TUBA

HUKUNCIN MAI KOMAWA CIKIN ZUNUBI BAYAN YA TUBA : TAMBAYA TA 2483 ******************** Salamun alaikum . ALLAH ya karawa mlm lfy, tambayata anan itace mutum ne yake cin haram, ko kuma yake aikata aiki na haram duk lokacin da yayi sai ya ayyana azuciyarsa bazai kara yi ba, sai kuma ya kara yi. 1. Menene hukuncin hakan ? 2. Shin wacce irin shawarwari ya kamata mutum yabi domin kubuta daga hakan?. Nagode bissalam. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Yawan komawarsa cikin zunubi ba zai sa Allah ya dena karbar tubansa ba. Tunda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "ALLAH YANA KARBAR TUBAN BAWANSA MUTUQAR BAI JE GARGARA BA". (Wato mutuqar bai je lokacin fitar rai ba). Sharudan da suka kamar ya kula dasu duk sanda zai tiba sun ha'da da : - Yin nadama bisa laifukansa na baya. - Daukar niyyar cewa har abada ba zai sake komawa cikin laifinsa ba. - Nisantar duk abinda zai iya kaishi ga aikata irin wannan laifin. - Mayar wa masu hakki hakkinsu, ko kuma neman yafewarsu. Daga karshe ina baka shawarar Kaji Tsoron Allah afili da boye, tare da yawan tunawa da ranar mutuwarka da kwanciyar Qabarinka da kuma hisabin da Allah zai yi maka aranar Alqiyamah. WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU (04-04-2018 19/07/1439).
Post a Comment (0)