27. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Muna cikin tafiya sai muka gamu da wani ayari za shi Gambiya. Mutanen suka ce mana wai za su su fanso wani ne da aka kama, aka ce in ba a kai fansarsa cikin 'yan watanni ba, za a sayad da shi a bauta. Suka sauke, aka yi zango a nan, aka shiga shirin girkin kalaci. Ashe ba mu sani ba, a lokacin mutanen Isyaku sun ga zuma, sai suka tasam ma sha. Mu dai ba mu farga ba sai muka ji harbi kurum ! Muka watse, dabbobi kuma suka fashe da mu da su kowa ya kama gabansa. Aka yi sa'a, a Iokacin duk an sauke wa jakuna kayansu, amma mutane da dawaki sun sha harbi da kyau. Wutar da aka hura don girki kuma ta kama ciyawar wurin, kafin a yi haka dajin duk ya kama wuta. Saura kadan dai da kayammu sun ci wuta. Kai, sai dai da aka yi wajen sa'a guda kana zuman nan ta lafa, muka sami damar zuwa wurin kayan. Muka bazu cikin daji, muka rika kamo jakuna da dawaki da dai dai. Jakuna uku suka bace, daya kuwa ya mutu da maraice, daya ya bi shi da safe. Watau dai jakuna shida muka rasa. Dokin Isyaku kuma ya bace, amma da dare an samo shi a daji.
Da muka tashi sai wani gari wai shi Badu. Nan har na sami wadanda za su tafi Gambiya na rubuta takarda zuwa ga matata a Ingila, na ba su. Ga takardar :
Badu, 29 ga Mayu 1805.
Masoyiyata,
Gaisuwa mai yawa, Bayan haka ina farin ciki in shaida miki mun ci rabin tafiyarmu, babu kuwa wani hadari ko tashin hankali. Dukammu lafiyarmu kalau. Na gamu da abokaina, da idon sani da yawa, kuma ko'ina ana karbar bakuntata da kyau. Ina zaton zuwa 27 ga Yuli za mu kare tafiya a kasa, sai kuma mu shiga ruwa. To, ran da fa muka ga mun fara tafiya a kan ruwan Kwara sai mu sa zuciyar komowa Ingila nan da nan. Tun da na fito, ko ciwon kai ban taba yi ba, Alexander kuma yanzu ya bar kukan ciwon cikin nan nasa.
Ba zan tsawaita zance ba, don kuwa wanda zai kai takardan nan Gambiya wani farke ne, ga shi tsaye da jakunansa yana jira, ya kuwa kosa ya wuce. Saboda haka ina so ki fada wa abokai duka muna nan lafiya, tafiya kuwa sai gaba ta ke yi. Yadda al'amar'm ke tafe babu wani tashin hankali haka, ban ga dadewarmu a cikin Afirka za ta kai yadda na zata ba.
Ko‘ina da guzurimmu mu ke tafe, babu yunwa ba kishirwa. Da ma kuwa wajen abinci muka fi tsoro, amma ga shi babu wata wahala.
Ina dai fata da ke da ’ya‘yana da abokaina duk kuna lafiya. Ina nan ina fatar kare wannan tafiya cikin ’yan watanni kadan tare da biyan bukata. In haka ya samu, babu abin da zai faranta mini zuciya kamar in ga na sa fuska na nufo Ingila. Wane irin farin ciki zan yi a ran nan, oho ! To, ga farke fa ya kosa ya yi gaba, saboda haka zan tsaya nan.
Ni Ne Masoyinki, Mijinki.
Ga mu nan muna tafiya, har muka shiga kasar Futa Jallon. Garin da muka fara isa a wannan kasa shi ne Julifunda. An ce mutanen garin da Arna ne, sai da Sarkin Futa Jallon ya yake su sa'an nan suka Musulunta. Sarkin Julifunda, Mansa Kussan, shahararren mugu ne, ya fi kowa tare ayari ya dibga musu kudin fito, in kuwa sun ki biya ya washe su. Da maraice ya yi sai na aiki tafintammu Isyaku, na ce ya je ya yi mini gaisuwa. Na ba shi duwatsu da jan zane, na ce a kai wa Sarki, a kuma gaya masa ina so in kwana daya a garinsa, gobe in wuce. Ya yi murna, ya nuna ya gode a fili, har ya yi mana addu’a, ya ce zai taimake mu, mu fita kasarsa lafiya. Ashe ta zuci na zuci, mugun na shirin yin halinsa !
Da gari ya waye na tura masu jakuna gaba, da ni da Mr. Anderson kadai ke baya, sai dawakimmu. Muka aika a shaida wa Mansa Kussan mun yi harama. Da dan sako ya dawo, sai ya ce wai Sarkin ya ce im muka kuskura muka tashi ba mu ba da kudin fito a kan duk abin da mu ke dauke da shi ba, zai sa a tsare mu a daji a kwace kayammu.
Da na ji haka sai na sa aka bi sawun ayari, na ce su komo. Na sake aika wa Sarkin da jar tufa, amma ni na ki tafiya gare shi da kaina. Na ji tsegumin wai yana so ya kama ni ya tsare, sai mutanena sun ba da fansa mai yawa kana ya sake ni. Har wa yau dai kwadayinsa bai lafa ba, sai da ya kwace wani jaki da na saya a garin, na kuma aika masa da su bindiga, da takobi, da dai 'yan tarkace da yawa. Da aikawa da wadannan sai kanensa ya zo ya ce mini yanzu sai in saki zuciyata, don Sarki ba zai sake neman wani abu ba kuma.
Da Isyaku da kanen Sarki suka tafi gari don su kai wa Sarki kayan nan, ni kuma na sa haramar tafiya. Can sai ga su sun komo, suka ce wai Sarki ya ce bai yarda in tafi ba sai na ba da albarushi da kyastu an kai masa. Kai, Sarkin dai ya kure ni ainun ! Sai na ce Isyaku ya gaya wa kanen ya je ya gaya wa wansa ba zam bayar ba. Irin abin da na bayar ya isa. Ko ya gode ko kada ya gode, duka daya. Kuma in bai bar ni na shige kasarsa da girma da arziki ba, zan shige ko da halin kaka! ln kuwa ya tura mutanensa su tare mu a daji, to, kome ya same su, su kuka da kansu. ‘Yan’uwan Sarkin da fadawansa suka matsa sai dai in aika da albarushin, ko wani abu dabam. Na ce musu mu, a al'adarmu ta Turawa, gwamma mu yi kasada da kayammu, da mu bari a kwace mana ta hanyar zalunci.
Aka fa kai aka komo, aka yi ta dauki-ba-dadi, sa ’an nan aka ce wai Sarki ya yi murna da abin da na bayar. Abin ma da ya kara ba ni mamaki, shi ne da aka ce wai har yana zuwa gare ni don mu yi sallama da azahar. Lokacin na yi kuwa sai ga shi. Fadawa sun dafo bayansa, a gabansa ga wata zabiya tana tafe tana rera waka, tana juyawa, tana nuna shi, tana kirari. Da zuwa, bayan mun gaisa, ya sa aka ba ni goro. Na ce Isyaku ya karba ya ci. Ya kuma ba ni mutum guda, ya ce ya kai ni har iyakar kasarsa sa’an nan ya komo. Muka dai yi sallama muka rubu, na tashi 4 ga Yuni 1805.
To, ran nan kuwa ranar haihuwar Sarkin Ingila ke nan. Saboda haka, da muka isa Banisarile, sai na sa aka shirya shagali don girmama wannan rana. Na sayi wani hurtumin bajimi da maraki, aka yanka wa Soja. Suka soya, suka dafa, suka gasa, aka yi ta nashadi. Da rana ta karya, na ce duk soja su yi holi. Da suka yi, aka ba su oda suka yi maci, aka yi ta rusa bindiga. Kai, muka dai yi duk abin da za mu iya don mu ji dadin wannan rana. Kuma ko da ya ke ga mu cikin wannan halaka da wahala haka, amma ko wadanda ke Ingila ba su fi mu roka wa Sarkin Ingila nasara da tsawon rai ba. Mutanen Banisarile Musulmi ne, kuma Sarkin garin kafin a sami mutumin kirki irinsa sai an tona. Na ba shi Linjila wadda aka rubuta da Larabci, ya yi murna kwarai da gaske.
Kashegari muka yi gaba. A hanya wani kafinta Bature cikin mutanena, ana kiransa James, ya kasa. Yana fama da atini, ba ya iya ko zama kan jakinsa. Tilas na sa wadansu soja su rika shi a kan jakin kada ya fado. Da ciwo ya ci karfinsa sai ya debe zuciya ga warkewa, ya sa rai ga mutuwa. Ko an rika shi a kan jakin sai ya kwace ya fado kasa. Kai, har dai ya ce shi a bar shi, ya gwammace ya mutu. Da dai na ga zai hana mu sauri, kuma ga alama mutuwar zai yi, sai na bar shi a wani kauye. Na sa shi a hannun sarkin garin, na ba da abin likkafani, na ce in ya mutu a binne shi, mu kuwa muka wuce. Kashegari da safe sai ga yaron sarkin ya zo ya gaya mana wai James ya rasu tun jiya da yamma.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada