ME CIKI KO SHAYARWA NA IYA AJIYE AZUMI?

*```SHIN ME CIKI KO ME SHAYARWA TANA IYA IJE AZUMI? KUMA IN TA IJE AZUMIN SHIN AKWAI RAMUWA AKANTA KO BABU?*```

*_TAMBAYA TA 1079:_*                                                                                           🕋🕋🕋🌟🌙
_DAGA ZAUREN_
*_📚MATA MUMINAI_*📚

ASSALAMU Alaikum mlm Ya kokari Allah ya saka muku da alkhairi
Malam inada tambaya ne akan ciyar da azumi malam inada juna biyu kuma inada ulcer nasan in banci abinci ba ina shan wahala to malam idan banyi axumi ba zanzo na rama ne ko zan ciyar se ayita cewa wai sai ka rama Dan Allah malam a taimake mun da cikkaken bayani akan haka na gode

_*AMSA*_

_*WA'ALAIKUMUSSALAM....*_

To wannan Tambayar za fahimci Amsantane dakyau in an fahimci wadannan Mas'aloli guda 3 (uku) masu zuwa:⤵

*_MAS'ALA TA 1:⤵_*
Azumi afarkon Muslinci yakasance anayinshine na ganin dama,wanda yaga ze yi yayi wanda kuma bayasonyi se ya ciyar da Miskini kawai shikenan. Shine fadin Allah S.W :⤵
*ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻄِﻴﻘُﻮﻧَﻪُ ﻓِﺪْﻳَﺔٌ ﻃَﻌَﺎﻡُ ﻣِﺴْﻜِﻴﻦٍ ﻓَﻤَﻦْ ﺗَﻄَﻮَّﻉَ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻓَﻬُﻮَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَﻪُ ﻭَﺃَﻥْ ﺗَﺼُﻮﻣُﻮﺍ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَﻜُﻢ*ْ
*ﺇِﻥْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ . ‏( 184 Baqara)*

*MA'ANA*:⤵
```"Kuma wadanda bazasu iya yinshiba (Shi Azuminkenan) akansu akwai cida Miskini,Amma duk wanda yayi Tadawwi'i na Alkhairi (yayi Azumin) to wannan Alkhairine agareshi......."``` _Baqara ayata 184_

Ibn Abi Laila ya Ruwaito daga sahabbai cewa wannan ayan ta saukane akan Sahabbai cewa duk wanda Azumi ze bashi wahala to yaciyar da miskini kawai kuma baze rama Azuminba. _Bukhari 8/135, Baihaqi 4/200, Abu Daud 507, Tagliqutta'aliq 3/185_

To wannan Ayar tasa duk sahabbai suka bar yin Azumi,kowwa se ya dinga ciyarwa kawai,to dagabaya se Allah ya saukar da wannan ayan akancewa kowwa yanzu wajibine yayi Azumi:⤵

*_MAS'ALA TA 2:⤵_*
*ﻓَﻤَﻦْ ﺷَﻬِﺪَ ﻣِﻨْﻜُﻢُ ﺍﻟﺸَّﻬْﺮَﻓَﻠْﻴَﺼُﻤْﻪُ ﻭَﻣَﻦْ ﻛَﺎﻥَ ﻣَﺮِﻳﻀًﺎ ﺃَﻭْ ﻋَﻠَﻰ ﺳَﻔَﺮٍ ﻓَﻌِﺪَّﺓٌ ﻣِﻦْ ﺃَﻳَّﺎﻡٍ ﺃُﺧَﺮَ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻴُﺴْﺮَ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ﺑِﻜُﻢُ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮَ ﻭَﻟِﺘُﻜْﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟْﻌِﺪَّﺓَ ﻭَﻟِﺘُﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻫَﺪَﺍﻛُﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ ﴾*[ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 185 ‏]

*MA'ANA:⤵*
```"Duk wanda ya halarci Watan (Ramadan) to ya Azumceshi,kuma wanda beda lafiya ko wanda yake kan Tafiya to ya Rama acikin kwanaki na gaba...."``` _Baqara ayata 185_

Se sahabbai kaman Abdullahi bn Umar da Salamah bn Akwa'a sukace wannan ayan ta mas'ala ta biyu ta shafe (ta goge) hukuncin waccan Ayan ta mas'ala ta farko. _Bukhari 4/188 dakuma 8/181, Muslim 1145_

✅Amma abin lura shine:In sahabbai sukace AN SHAFE AYA to ba dole suna nufin Anshafeta dukaba, A'a, koda anshafe wani yanki ko wani sashi na ayane to sunacewa Anshafe Ayan. _Duba ciki littafin I'ilamul muwaqqi'in na Ibnil Qayyim, dakuma Al-Muwafiqat na Imam Shatibi._

*_MAS'ALA TA 3:_⤵*
✅Danhaka su Sahabban sukace wannan shafewan da akayi ba gabadaya ayan aka shafeba,danhaka haryanzu ayan tayi Sauqi ga mutane 2,sune: Tsoho ko Tsohuwa dakuma Me Ciki (juna 2) ko me Shayarwa in sunji tsoron wani Abu ga yaronsu ko garesu,dukkansu zasu sha Azumi kuma babu Ramuwa akansu. _Haka Ibn Abbas yace kaman yanda malamai suka ruwaito. Ibn Jarud 187,Baihaqi 3/230,Abu Daud 2318._

Haka ibn Umar yace: "Me ciki ko me Shayarwa ciyarda Mudunnabiyyi zasuyi na Alkama" _Imam Daru Qutni ya ruwaito 1/207_

Hakama Annabi S.A.W yace: " ```Allah ya dauke ma Matafiyi Rabin Sallah,kuma ya dauke ma Me Ciki ko me Shayarwa Azumi``` ". _Tirmizi 715,Nisa'i 4/180, Abu Daud 2408, Ibn Majah 1667._

Kai hakadai Ibn Qudama yace: "babu wanda ya saba daga cikin Sahabbai akancewa masu Ciki da masu Shayarwa Zasu iya shan Azumi suyi ciyarwa. Almugni 3/21.

*ATAQAICE:⤵*
Masu Ciki ko Masu Shayarwa in sunji tsoron Wani Abu ga yaransu ko ga su kansu to ciyarwa zasuyi kuma babu ramuwa akansu.

_Allah yasa mudace._.
.
*_📝Amsawa:-📚_*
_Malam Yusuf Salisu Kaduna_
_*~Via~📚 MATA MUMINAI 📚*_
*+2348108407420*
*+2347033537189*
*+2347035269582*
Domin kasancewa damu ta shafinmu na facebook se abi ta wannan hanyar a shiga ayi like
https://www.facebook.com/MATA-muminai-1841397762846865/

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anla ilaha illa anta astagfiruka wa'atubu ilaika".

Post a Comment (0)