TARBIYYA WAJIBI CE GA IYAYE

TARBIYYA WAJIBI CE GA IYAYE





 Malaman tarbiya sunfadi wasu Abubuwa kamar haka:
1-Zagin Yaro Kullum nasa ya lalace.
2-Tsangwama ga Yaro na jawo masa rashin walwala.
3-Kushe Yaro kullum nasa shi ya raina kansa.
4-Kunyata Yaro nasa shi yadinga dari-dari da kansa.
5-koyawa Yaro Juriya nasashi yazama mai Hakuri.
6-Idan ana yaba Yaro yakan tashi da kishin zuci.
7-Idan ana kyautatawa Yaro yakan sanyashi yazama mai gaskiya.
8-tarbiyya ga Yaro takan sanyashi yazama amintacce.
9-Idan aka amince da Yaro yakan sanyashi yaji dadi.
10-Sakin fuska ga Yaro shike jawo shi cikin Jama'a.

 Allah ya sakawa Iyayen mu da alheri bisaga tarbiyyar da suke bamu, ya kara musu lfy da imani, ya yafe musu kurakurensu, ya jikan wadanda suka rasu cikinsu.
Post a Comment (0)