ALLAAH YA SANYA TSAYAR DA ADALCI A BAYAN ƘASA...

Allah Ya Sanya Tsayar Da Adalci A Bayan Kasa Ya Zama Sharadin Samun Zaman Lafiya Da Cigaba Mai Dorewa!

Daga Imam Murtadha Gusau

Talata, 12 Mayu, 2019

Bismillahir Rahmanir Rahim

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna yabon sa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah da kariyarsa daga sharrin munanan ayyukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad, bawan sa ne kuma Manzon sa ne. 

Salati da sallamawa da tsira su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da matansa da duk wanda yayi imani da shi kuma yayi aikin kwarai har zuwa ranar tashin kiyama.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Ku sani, lallai Allah Ya umarce mu da tsayar da adalci a bayan kasa, kuma ya sanar da mu cewa, da adalci ne sama da kasa suka tsayu. Kuma shine ginshiki da tushen samun zaman lafiya da cigaba masu dorewa a cikin al'ummah. Sannan nagartattun malamai, salihan bayin Allah, irin su Shaikhul Islamu Ibn Taimiyya da Sheikh Usman Dan Fodio da Malam Abdullahin Gwandu sun shaida muna cewa:

"Allah yana taimakon daular da ta tsayar da adalci koda kafira ce, a yayin da Allah yake durkusar da daular da take zalunci koda Musulmi ke shugabancin ta."

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Darasin mu na yau yana bayani ne akan muhimmancin adalci, wanda a yau mu al'ummar Musulmi yake neman yayi karanci a tsakanin mu.

Allah Madaukaki Ya umurci Musulmi da su tsai da adalci ta kowane hali, inda Yace: 

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku akan ba zaku yi adalci ba. Kuyi adalci shine mafi kusa da takawa.”

Kuma Allah Yace: 

“Kuma idan kun fadi magana to kuyi adalci, kuma koda ya kasance ma’abaucin zumunta ne….”

Kuma Allah Ya sake cewa:

“Lallai Allah Yana umurninku da adalci da kuma kyautatawa…”

Kuma Allah Yace:

"Hakika mun aiko Manzannin mu da hujjoji bayyanannu, kuma mun saukar masu da littafi da ma'auni (na tsayar da adalci) domin mutane su tsayar da adalci tsakaninsu..."

Kuma Allah ya fada a Hadisil Qudusi cewa:

"Na haramta zalunci ga kaina, kuma na sanya shi ya zama haramun a tsakanin ku, saboda haka kada ku zalunci junanku."

Ya ku Jama'a! Adalci shine, bai wa kowa hakkinsa da Shari'a ta tabbatar masa, ba tare da nuna ko wane irin banbanci ba. Kuma duk inda ake tsayar da adalci, to lallai zaka samu zaman lafiya, son juna, walwala, cigaba da jin dadi a cikin al'ummah da tsakankanin jama'ah sun yawaita. A Musulunci, tsayar da adalci yana daga cikin manyan kyawawan dabi'u. Wannan ya nuna kenan duk inda Musulmi suke, indai har Musulmin gaskiya ne, to zaka same su sun rungumi adalci.

Kuma Alkur'ani Mai girma ya bayyana karara cewa Allah ya umurci mutane da dukkan al'ummomi masu neman zaman lafiya da cigaba, su mu'amalanci juna da kyakkyawar mu'amala, tausayi da tsayar da adalci a duk halin da suka samu kansu a ciki. Kuma kowa yana sane da cewa, Allah yana son adalci, kuma yaki jinin zalunci, kuma baya son azzalumai.

Ya ku bayin Allah! Lallai ku sani, Allah ya wajabta wa dukkanin mutane, suyi kokari wurin ganin cewa an tabbatar da adalci a bayan kasa, domin samun zaman lafiya mai dorewa. Shi yasa Allah ya aiko Annabawa, kuma ya hado su da dokoki, domin su taimakawa mutane wurin tsayar da adalci. Wahayin da suka karba daga Allah ya nuna hanyar da za'a bi a tsayar da adalci a cikin al'ummah. Misali, yiwa talakawa adalci, maza da mata, kai hatta makiyan mu an umurce mu da yi masu adalci.

Wajibi ne Musulmi su hadu, su hada kai domin su dakatar da rashin adalci da zalunci a cikin al'ummah. Wannan aiki ne da Allah ya dora masu. Abune da sam bai dace ba Musulmi su zuba ido, su rungume hannuwansu, suna kallo ana tafka zalunci da rashin adalci ba tare da sun dauki matakin da ya dace wurin tsayar da shi ba.

Ya ku 'yan uwana masu albarka! Kamar yadda kuka sani, aiki da dokokin Allah da shari'arsa wajibi ne a wurin dukkan Musulmi ta ko wane hali. Sannan duk Musulmi yasan da cewa siyasa ta kasu kashi-kashi, akwai siyasar Musulunci sannan akwai wadda ba ta Musulunci ba. Misali, siyasar Dimukradiyya ai ba tamu bace mu Musulmi. Domin a Musulunci muna da tamu siyasa, wato ta Shari'a. Kawai mun samu kan mu cikin wani yanayi ne mu Musulmin Nigeria. Sai aka wayi gari muna yin siyasar Dimukradiyyah a bisa lalura. Wannan tsari na Dimukradiyyah, bakon tsari ne a Musulunci, da muka amince muyi shi, amma a bisa lalura. Kenan ya zama wajibi in dai har muna son zaman lafiya mai dorewa a tsakankaninmu, muyi wannan tsari a bisa dokokin sa da tsarin sa da masu shi suka tsara shi a kai, na ganin cewa duk wanda yaci a bashi, wanda Allah ya ba a bashi, kar ayi wa kowa kwace da nuna fin karfi! Domin matukar aka kaucewa wannan, to lallai zamu jefa kan mu cikin tashin hankali, fitina da rudani. Allah ya kiyaye, amin.

Ya ku bayin Allah! Bari in tambaye mu don Allah, shin yanzu abubuwan da suka gudana a wannan kasa tamu mai albarka Nigeria, na zaben da aka gudanar na Gwamnonin jihohi, shin akwai niyyar tabbatarwa da wasu adalci kuwa? Amsa ita ce: ga alamu, a'a.

Kuma shin me yasa ne dukkanin jihohin da akace zabe bai kammala ba, jihohi ne da ake ganin jam'iyyar adawa ta PDP ta ke kan gaba? Shin me ake shirin yi anan? Shin ana son a murde masu ne? Shin ana da niyyar tabbatar da adalci a wannan al'amari? Amsa dai ita ce: bamu ga alamun hakan ba!

To wallahi, muna kira da babbar murya, kuji tsoron Allah, kar ku jefa mu cikin rikici da tashin hankali! Don Allah duk wanda Allah ya ba mulki ku bashi, kar kuce zaku murde, ku hana masa. Kuyi wa kowa adalci. Wannan shi zai sa mu samu zaman lafiya da cigaba mai dorewa.

Ina mai girma Shugaban kasar mu Muhammadu Buhari? Kar kayi shiru akan wannan al'amari, kasa baki don Allah, ka nuna masu duk wanda Allah ya bai wa a bashi. Ka tuna fa, kirarin ka shine MAI GASKIYA. Kar ka bari wasu miyagu su bata maka tafiyar ka. Yi kokari yadda ka fara lafiya ka gama lafiya! Kar ka yarda a danne hakkin wasu. Ka sani, Allah yana kallon ka, sannan duniya tana kallon ka!

Ina kwamitin zaman lafiya na su mai girma tsohon shugaban kasa AbdulSalam Abubakar, su Mai Alfarmah Sultan, su Reverend Matthew Hasan Kuka, su John Onaiyekan? Ya kamata ku sa baki a cikin wannan al'amari, ku tabbatar da cewa duk wanda yaci zabe an bashi, domin tabbatar da samun zaman lafiya a kasar mu mai albarka, Nigeria.

Ina Sarakunan mu suke? Kune fa iyayen wannan al'ummah! Ya zama wajibi ku bada gudummawar ku wurin ganin an kaucewa tashin hankali. Duk wanda Allah yasa yaci zabe a bashi hakkinsa.

Ina Malaman mu na Musulunci? Shin kun manta da umurnin Allah na tsayar da adalci?

Ina Fastoci suke? Shin ina zancen tabbatar da adalci da kuke karantawa a littafin ku?

Duniya fa tana kallon abunda yake faruwa a Nigeria! Kuma dukkanin mu muna sane da illar da rashin adalci yake haifar wa mara dadi. Don Allah mu hadu muyi wani abu akai.

Irin abun da muke gani, da abubuwan da suke faruwa, yanzu dai kam babu wata Dimukradiyyah a Nigeria. Misali:

1. A Jihar Kano an ce zabe bai kammala ba, saboda jam'iyyar PDP ta adawa ce ke kan gaba!

2. A Jihar Sokoto an ce zabe bai kammala ba, anan ma PDP ce ke kan gaba!

3. A Jihar Plateau ma an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba!

4. A Jihar Adamawa an ce zabe bai kammala ba, nan ma PDP ce ke kan gaba da kuri'u mafiya rinjaye!

5. A Jihar Bauchi an ce zabe bai kammala ba, nan ma don sun ga PDP ce ke kan gaba!

6. A Jihar Benue ma haka, sun ce zabe bai kammala ba, saboda Jihar PDP ce!

7. Haka abun yake a Jihar Rivers, an dakatar da duk wasu harkokin zabe, saboda Jihar PDP ce!

Amma saurara kaji wani abun mamaki, ikon Allah:

1. A Jihar Kaduna an ce zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

2. A Jihar Niger zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

3. A Jihar Kebbi, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

4. A Jihar Katsina, nan ma zabe ya kammala, saboda APC ce ta lashe zaben!

5. A Jihar Gombe, zabe ya kammala, saboda APC tayi nasara!

6. A Jihar Jigawa, zabe ya kammala, nan ma saboda APC ce ta ci!

7. A Jihar Nasarawa, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

8. A Jihar Kwara, zabe ya kammala, saboda APC ce tayi nasara!

9. A Jihar Borno, anyi kammalallen zabe, domin APC ce ta cinye!

10. A Jihar Yobe, nan ma babu matsala, domin ta APC ce!

11. A Jiha ta Zamfara ma anyi kammalallen zabe, saboda jam'iyya mai mulki ta APC ta ci zabe!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Yanzu don Allah zaku gaya mani cewa, wannan abun gaskiya aka bi wurin tabbatar da shi? To in dai har ku kun yarda, ni dai kam wallahi, sam ban amince ba.

Maganar gaskiya wannan sharri ne da magudi da rashin adalci irin na 'yan siyasa. Kuma wadannan 'yan siyasar da ke kokarin tafka rashin adalci, wallahi, basa son zaman lafiyar Al'ummar su, musamman ma arewa. Suna son su jefa mu cikin wani sabon tashin hankali da rikici. Allah ya tsare, ya kiyaye, kuma Allah ya mayar masu da aniyar su, amin.

Don Allah me yasa ne duk inda jam'iyyar APC ta lashe zabe suka sanar da cinye zaben, amma kuma duk inda jam'iyyar PDP ta ke kan gaba suka ce wai ba'a kammala zabe ba?

Kuma wai a haka ne za'a gaya muna wai ana yin Dimukradiyyah. Wace Dimukradiyyar kenan? Dimukradiyyah ko dai yaudara?

Wallahi bai kamata ku rinka wahalar da jama'ah ba, matukar kun san kama karya da rashin adalci zaku yi. Yanzu don Allah abunda ya faru a Kano ba abun kunya bane? Ace irin wadannan mutane sune suke jagorantar al'ummah Musulma irin Kano?

Muna Addu'a Allah ya ceto yankin mu na arewa da Nigeria baki daya, daga sharrin da wadannan mutane ke kokarin jefa su, amin.

Ta yaya zaku ce kuyi amfani da karfi ku kwace mulki daga hannun wadanda Allah ya bai wa, sannan kuce kuna son zaman lafiya? Zaman lafiyar naku ne? Ba Allah yake da shi ba? Sannan ya baku idan kun tsayar da adalci?

Amma babu komai, ku da Allah, da kuma jama'ar Nigeria masu kokarin ganin an tabbatar da adalci ga kowa da kowa!

Ya ku 'yan uwana masu daraja! Ina kara tunatar da ku, Allah Madaukaki Ya siffanta kan sa da cewa Shi Mai umurni ne da yin adalci, Mai kuma hanin yin zalunci ne. Yace a cikin suratun Nahl aya ta 90:

"Lallai Allah yana yin umurni da yin adalci, da ihsani, da yin kyauta ga ma'abucin kusanci, Yana hanin aikata alfasha, da munkari, da zalunci, Yana muku wa'azi kila za ku wa'azantu."

Sannan Ya haramta wa kanSa zalunci, ya kuma haramta wa bayinsa yin zalunci.

Sannan lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: haramta zaluntar Jama'a. Kuma lallai yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya shahara da shi: wajabta taimakon wanda ake zalunta.

Babu ta yadda za ayi Musuluncin mutum, da mutuntakar sa su cika matukar ba ya kokarin tunkude wa al'ummar sa zalunci da rashin adalci.

Sannan lallai abu ne da yake wajibi a kan dukkan wani mai iko, yayi dukkan abin da zai iyayi na halal domin ya tunkude wa al'ummar sa zalunci da aukuwar tashin hankali da fitina.

Imamul Bukhari ya ruwaito Hadisi cikin Sahihin sa daga Sahabi Anas Dan Malik Allah Ya kara masa yarda ya ce:

"Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace: "Ka taimaki dan uwan ka yana azzalumi ko yana wanda aka zalunta" sai wani mutum ya ce: Ya manzon Allah zan taimake shi in yana wanda aka zalunta (in kwato masa hakkinsa), to amma in yana mai zalunci ta yaya zan taimake shi? Sai yace: Ka hana shi yin zalunci wannan shine taimakon ka gare shi."

Sannan Imamu Muslim ya ruwaito Hadisi daga Sahabi Jabir Dan Abdullahi yace:

"Wasu yara biyu sun yi fada da juna, daya daga cikin Muhajirai yake, dayan kuwa daga cikin Ansarawa, sai Muhajirin ya daga murya ya nemi taimakon Muhajirai, shi kuwa ba'ansaren ya daga murya ya nemi taimakon Ansarawa, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya fito yace: Wane irin kirayen jahiliyya ne haka? Sai suka ce: Ya Manzon Allah yara ne biyu suke fada da juna, sai dayan su ya doki dayan su a duburarsa. Sai (Annabi) yace: Babu laifi, mutum ya taimaki Dan uwan sa yana azzalumi ko yana wanda ake zalunta, in ya kasance azzalumi ne sai ya hana shi yin zaluncin, wannan shine taimakon sa gare shi, in kuma ya kasance wanda ake zalunta ne sai ya taimake shi."

Sannan zunubi ne babba mutum ya ga ana kokarin wulakanta wasu muminai a gaban sa, kuma ya kame hannayen sa da bakin sa, ba tare da yayi wani yunkuri domin ya kawo masu agajin da zai iya ba.

Ya ku 'yan uwana Musulmi! Kuma yana da kyau ku sani, a dokokin Musulunci, da kuma aqidah da manhajin Ahlis-Sunnah wal Jama'ah, duk wanda Allah (SWT) ya ba mulki, ko ta wace hanya ne, kuma ko da baka so ya zama shugaba ba, to kayi hakuri, kayi masa da'a da biyayya, matukar bai umurce ka da sabawa Allah ba. Sannan kayi masa Addu'a da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci ga kowa da kowa, hatta wadanda basu tare da shi. Kuma kayi masa Addu'ar Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ya dora masa. 

Ya Allah, ina rokon ka, don tsarkin sunayen ka, kayi wa dukkanin shugabannin mu jagora akan tafarki madaidaici da ka yarda da shi, amin.

Wassalamu Alaikum... Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Nigeria. Za'a same shi ta: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Post a Comment (0)