ABUBUWAN DA AKE SO MACE TA FI MIJIN TA

*_ABUBUWAN DA AKE SO MACE TA FI MIJINTA DA SU._*

                          *Tambaya*
Aslkm, malam ya azumi dafatan kasha ruwa lafiya. WASU TAMBAYOYI NAKE ROKON Malam daya taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu. 1. SHIN MALAM Wai a kwai wasu abubuwa uku da ake so mata tafi mijin da zata aura dasu, sannan shima akwai abu guda uku da'akeso yafita dasu?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka akansu, DAFATAN MALAM YASANSU KUMA ZA'A TAIMAKAMIN DA Su. NAGODE

                              *Amsa*
To dan'unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku:
1. Ta fi shi a kyau.
2. Ta fi shi kananan shekaru.
3. Ta fi son shi, sama da yadda yake sonta.

Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku:
1. Ya fi ta kudi.
2. Ya fi ta ilimi.
3. Ya fi ta jarunta.

Ana so su hadu a abubuwa uku:
1. Ya zama akwai yaran da yake hada su.
2. Ya zama addininsu daya.
3. Ya zama dukkansu suna son tarbiyya.

Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za'a samu jin dadin aure.

*_DON NEMAN KARIN BAYANI KA NEMI SHIRIN DA NA YI A FREEDOM RADIO RANAR: 3 GA RAMADHAN 1434 HI, A SHIRIN NA MINBARIN MALAMAI._*

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)