AURAN KAFIRAI KAFIN SU MUSULUNTA INGANTACCENE

*_AURAN KAFURAI KAFIN SUN MUSULUNTA INGANTACCE NE!!_*

                         *Tambaya*
Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to yaya matsayin yayan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah yataimaka ameen

                           *Amsa*
Wa'alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi S.A.W bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure. Sahabban Annabi S.A.W da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta. 

In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa baban sa ba bayan ya musulunta.                     
Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti'i 12/239.

Allah ne mafi Sani.

13-09-1438
08-06-2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
___________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)