JINI YA ƁARKE MIN SABODA ANYI MIN WANKIN CIKI

*_JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKI?_*

                             *Tambaya*
 Assalamu alaikum Dan Allah inada tambaya macen da tayi bari aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata yadai baiyana jinin ciwo ne Shin zata dunga wanka ne lokacin da zatayi kowace sallah? Ko kuwa tsarki kawai zatayi lokacin sallah?   

                                  *Amsa*
To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala  ya yın kowacce sallah, saboda hukuncinsu daya da mai istihâlâ, kamar yadda Annabi saw ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a hadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin kowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.

Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u Addabi'iyya: 45.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)