BAYANAI GAME DA SALLAR WALHA


*SALLAR WALAHA (DUHA), LOKACINTA, YAWAN RAKA’O’INTA DA KUMA FALALARTA:*

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum dafatan malam yatashi lfy Allah yaqarawa malam lafiya da da almajiransa baki daya Ameen

Tambayata anan itace don Allah malam inaso ayimin cikakken bayani akan sallar wadha da lokacin yinta dalokacin fitatta wassalamu alaikum?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

_Lallai sallar walaha (duha) sunnah ce mustahabbiya mai falalar gaske._

_*Lokacinda ake yinta*_

_Lokacin sallar walaha yana farawa daga lokacinda hantsi ya fara wato lokacinda rana ta daga ta fara dan zafi har zuwa lokacinda tayi zawali ( wato lokacinda ta karkato daga tsakiyar samaniya) har kusan lokacin azzahar kenan._

_Shaykh Ibn Uthaymeen (a cikin Al-Sharh al-Mumti’i, 4/122) yace lokacin shine daidai misalin mintuna goma sha biyar (15mins) bayan rana ta fito har izuwa mintuna goma (10mins) kafin lokacin azzahar. Saboda haka duk wannan tsakanin lokacin duha ne._

_Saidai anfi son a jinkirta ta har zuwa lokacinda rana tayi zafi sosai saboda fadar Annabi (sallallahu alaihi wasallam) cewa: ” *Lokacinda aka fi son ayi sallar walaha shine lokacinda zafin rana yakai duk da ‘ya’yan raquma suna jin zafinsa*” Muslim (748), Ibn Baaz Majmu’u Fatawa (11/395)._

_*Raka’a nawa ake yi?*_

_Babu sabanin malamai a mafi qarancin adadin raka’o’inta sune raka’a *biyu*. Dalili kuwa shine Muslim (720), Abu Dawud da Ahmad sun ruwaito hadisi daga Abu Dharr (Allah ya yarda dashi) Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yana cewa: *”……. raka’o’i biyu wadanda dayanku ya sallata da walaha sun isar masa (sunyi daidai da wannan”*_

_Sa’anan kuma Al-Bukhari (1981) da Muslim (721) daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda dashi) yace: *”Masoyina (Annabi sallallahu alaihi wasallam) yayi min wasiyya da abubuwa guda uku: Azumin kwana uku a cikin kowane wata, sallar raka’o’i biyu da walaha da kuma yin wutiri kafin inyi barci”.*_

*Mafi yawan raka’o’inta*

_Akwai hadisai da dama wadanda suka gaya mana raka’o’in da Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yake yi a sallar walaha. Daga cikinsu akwai wadanda suka nuna yana yin hudu, wasu kuma su nuna yana yin takwas, wasu sha biyu, wasu kuma su nuna yana yin hudu kuma yana kara abinda yaso akan hakan da dai sauransu._

_To a bisa wannan dalilin yasa malamai suka samu sabani akan mafi yawan raka’o’in sallar walaha._

_A mazhabin *Malikiya* da *Hanbaliya*: suka ce mafi yawan raka’o’inta sune raka’o’i takwas sun kafa hujja ne da daya daga cikin hadisan ne wanda Ummu Hani (Allah ya yarda da ita) tace: *Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ya sallaci sallar duha raka’o’i takwas*. Muslim (336) ya ruwaito wannan hadisin._

_A mazhabin *Hanafiya* da *Shafi’iya*- a zance mafi inganci- da kuma Ahmad kamar yanda aka ruwaito daga gare shi su kuma sunce mafi yawan raka’o’inta sune raka’a goma sha biyu (12), su kuma sun kafa hujja ne da hadisin Tirmizi da Nasa’i da isnadi wanda yake akwai dan rauni a cikinsa wanda yace, Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace: *”Duk wanda ya sallaci sallar duha da raka’a takwas to Allah zai gina masa gidan zinari a aljannah”.*_

_To maganar karshe kuma zance mafi inganci da zama daidai shine qarancin raka’o’in sallar walaha sune raka’a *biyu* amma kuma bata da iyakar raka’o’i, saboda haka zaka iya yin ko raka’a nawa kake son yi daga *2, 4, 6, 8, 10, 12,…. har izuwa yanda kake iyawa a cikin lokacinta, a duk lokacinda kayi raka’a biyu ka sallama*. Dalili kuwa shine hadisin Aishah (Allah ha yarda da ita) tace *”Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana sallatar walaha da raka’a hudu, kuma yana qara abinda yaso akan haka”.* Muslim (719) da Ahmad da Ibn Majah suka ruwaito shi. Shaykh Ibn Baaz (a cikin Majmu’u Fatawa Ibn Baaz, 11/389) shima ya tabbatarda hakan yace basu da iyaka. Sunnah dai shine a duk lokacinda mutum yayi raka’a biyu ya sallama har yanda yaso. (Majmu’u Fatawa Ibn Baaz). Haka kuma Shaykh Ibn Uthaymeen (rahimahullah) shima (a cikin Sharh al-Mumti’i, 4/85) yace: raka’o’in basu da iyaka kuma ya kafa hujja da wannan hadisin na Aishah._

_Sa’annan kuma hadisi da isnadi mai kyau ruwayar Imam Tirmizi ya tabbatarda cewa Annabi yakan nace da yin sallar walaha har sai sahabbai sunce baya barinta, kuma yakan daina yinta har sai sunce baya sallatar ta. Saboda zaka iya yin hakan kai ma._

_*Falalar sallar walaha*_

_Hadisai da dama sun tabbata masu nuna dimbin falalar sallar walaha, amma yanzu zamu kawo falalolin a takaice kamar haka:_

_✒ Wanda yai sallar walaha raka’a takwas Allah zai gina masa gidan zinare a aljannah. Sahihu jami’u 6340._

_✒ Mai yin sallar walaha yana samun ladar wanda yayi umara. Sahihul jami’u 6228._

_✒ Yin sallar asubah a jam’i mutum ya zauna a inda yayi sallar yana ta zikiri har lokacin duha yayi sa’annan ya sallace ta yana da ladar aikin hajji da umara cikakku. Sahihul targib 469.

✒ Sallar walaha wasiyyar Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ce ga sahabbansa. Bukhari (1981) Muslim (721)._

_✒ Wanda yayi sallar walaha raka’a hudu a farkon yini, yana cikin ta musamman har zuwa yammaci daga Allah (subahanahu wata’ala). Sahihul Targib 671._

_Wannan shine cikakken takaitaccen bayanin sallar walaha (dhuha) daga zauren Tambayoyin Musulunci Whatsapp. Allah ya bamu ikon dabbaka wannan sunnar mai falalar gaske._

*Wallahu A’alamu.*

_Wanda ke son fadada bincike sai ya binciki wadannan littafai da hadisan da yake ganin muna kafa hujja dasu a cikin rubutun._

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب 
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕

2 Comments

Post a Comment