Mai TAKABA Zata Iya Fita Sallar IDI?

*_MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?_*


                                *Tambaya*
Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka. Don Allah YA halatta me takaba ta je sallar Eid?


                                   *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Bai halatta ga mai takaba ba ta fita zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031) inda Annabi S.A.W yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya Rasu: (Ki zauna a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar mijinki har zuwa Ki kammala iddarki" 

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba za ta fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a shari'a.
Imamu Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi bayani cewa "Dukkan Mata ana fitar da su daga gidanjansu Don su halarci idi, in ban da wacce take iddar mutuwa".

Allah ne mafi Sani.

03/09/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- ΓƒbΓ»bΓ€kΓ₯r ÊkΓ’.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren πŸ”‘ *_MIFTAHUL ILMI_* πŸ”‘ (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)