MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA, A WATAN RAMADANA?

*_MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA BAYAN ASUBA, A WATAN RAMADANA?_*


                                *Tambaya:*
Assalmu alaikum, malam ina da tambaya shin meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin azumi, amma ba zasuyi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin yaya matsayin azumin su yake? Nagode.


                                    *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan Ramadhana, a zuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi (S.A.W) yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalansa A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.

Allah shine mafi sani.

01/9/1438
27/5/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- ΓƒbΓ»bΓ€kΓ₯r ÊkΓ’.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren πŸ”‘ *_MIFTAHUL ILMI_* πŸ”‘ (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)