23. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Ko da ya bude baki, bai ce mini shai’an ba, sai ya shiga magana da majalisarsa. Ya ce musu, “Tun ran da Abdulkadir ya shiga hannummu na ke fada masa zuciyarsa ta bar rudinsa. Ba shi da abin yi illa ya ba da gaskiya gare mu daga baka har zuci, amma bai yarda ba. Na dauki Abdulkadir kamar dana na cikina ne, amma shi kullum tsakaninsa da ni sai dungu.” Ya juyo kuma gare ni ya ce, “Abdulkadir, mu Larabawa a karin maganarmu mu kan ce, “Duk inda ka ga hayaki, da wuta a wurin.” Naka hayakin kuwa ya yi yawa har ya murtuke. Manzo ya zo mana nan jiya daga Masar, ya ce kai dan rahoton hukumar Masar ne. Masar tana aiko maka da albashi ladan aikin da ka ke mata na rahoto, har ya ga baucar da ka sa hannu a ofishin wakilin kasarku ta Austria, wanda ke Masar. Ya ce kun yi kulli da hukumar Masar za ka koma bayansu in sun kawo mana yaki, har ma za ka nuna musu taskokimmu na harsashi. Wannan zance kuwa yana da kanshin gaskiya tun da ya ke taskar harsashi a kusa da gidanka ta ke. Amma duk da haka, sabo da amincewa da na yi da kai a zuciyata, ban gaskata mai ba da wannan labari ba, har na kama shi na daure. To, amma ko kana da hujjar munafuntarmu har ka rika kai rahotommu, bayan mun jawo ka a jikimmu haka ?"
Da jin wannan sai na natsu a zuciyata na ce, “Ya ubandakina, ina roko ka saurari hanzarina da kunnuwan adalci. Ni ba dan rahoto ba ne, karya a ke mini. Ba ni da wata hulda da hukumar Masar, balle a ce har tana biyana albashi. ’Yanuwana, barorinka, sun san asirina kaf, sun san irin wahalar da na ke sha wajen ciyad da iyalina. Mutumin da ke da albashi ya zauna da yunwa haka ? Kuma don ka tabbata wannan kullekulle ne na 'yanubanci, ta yaya mutumin nan ya san sa hannuna tun da ya ke bai iya karatun Turawa ba? In kuwa yana musu, a kawo shi nan in rubuta sunaye da dama har da nawa, a gani in zai iya nuna sunana. Ka fa tuna, ya Halifa, Sudan ce nan, ba Masar ba. Ka tuna kuma mutumin nan daga wurimmu ya gudu ya tafi Masar. Ashe in da wani dan rahotonka, shi ne. Im ba ta bakinsa ba, yaya hukumar Masar ta san karfinka, har ta san taskar harsashinka tana kusa da gidana ne ? Sai ka sa adalci, ka dubi wannan al'amari da kyau, ka gane mai gaskiya.
“Ni, abin da zuciyata ta karfafa, shi ne ba hukumar Masar ba, duk wata hukuma ma ta duniyan nan, ba mai iya karawa da kai, tun da ya ke su karfinsu na bindiga ne, kai kuwa naka na Ubangiji ne. In ko da yaki zai tashi tsakaninka da Masar, ka tabbata ni gurina daya ne, in ga ina sahun gaban sojojinka, in yi mutuwar shahada. Kuma shi wannan manzo ai yana da kulli a zuciyarsa game da ni. Don wata rana sun , taba zuwa nan da ubangidansa Nejumish Shahid, ya rika kankamba da neman wuce wuri, har ya tasam ma shiga gabanka ba da iso ba. Ganin haka ni kuwa na tura keyarsa waje. Wannan abin shi ya ke rike da shi a zuciyarsa, don haka ya ke neman daukar fansa ta shirya wannan makirci gare ka. Mancewa ya yi Allah ya ba ka hikima da adalci wanda bai ba duk wani dan Adam ba. Hikiman nan da adalcin nan su na ke roko ka yi aiki da su wajen duba wannan al’amari. Iyakar hanzarina ke nan.”
Ba Halifa ba, ko Shaidan kansa, wannan jawabi zai raunana zuciyarsa. Ko da na cira ido na dube shi, sai na ga lalle zancen ya ratsa shi sosai. Aka yi shiru shiru duk wurin, sa’an nan zuwa can Halifa ya ce, “Abdulkadir, ni ba kiranka na yi don in hukunta ka ba, na kira ka ne in nuna maka ni na yarda da kai a cikin raina, ko da ya ke ’yanuba kullum suna ta saranka. In da ina yarda da tsegunguman mutane, ai da yanzu kashinka ya yi fari. Na sani kana da magabta da yawa, tumbana da su ke ganinka bako, suka ga kuma ka zama dammorina. Amma duk da haka ka kara kulawa, kada fa ka manta ruwa ba ya tsami banza, ba a hayaki sai da wuta. Tashi ka fita.” Na fice.
Na tabbata tun ran da Halifa ya ke, bai taba yarda da ni ba, amma yanzu al’amarin rashin yarda tsakanimmu ya kai matuka. Kashegari ina zaune, bayan na komo daga fada, sai ga sako wai in kwashe kayana karkaf in tashi, an sake mini gida can kusa da na Halifa. Wannan ya nuna mini Halifa ya yarda da zancen mutumin nan ke nan, watau ni dan rahoton Masar ne. Da ya ke kuwa gidana yana kusa da taskar harsashi ne, lalle im Misirawa suka kawo yaki zan nuna musu wurin. Na dai kwashe tarkacena da barorina, na koma sabon gida.
Malam mai karatu, kada dai in cika maka dogon zance. In na ce zam fada maka halayen Halifa Abdullahi ne, da dabi’o’insa munana, sai in cika littafi uku kamar wannan ban kome na karewa ba. Sabo da haka kila in na ce duk mugun da ka sani a duniya, duk maci amanan da ka sani, duk mai kishin da ka sani, kuma duk matsoracin da ka sani, Halifa Abdullahi ya wuce shi, za ka iya gane irin mutumin da na ke tsare a hannunsa. Yanzu abin da ya fi kyau, shi ne in ci gaba da bayyana maka yadda mulkin Halifa ya rude, da yadda na yi har na sami tserewa daga Sudan, na sami ’yancina.
An sani ko lokacin da hukumar kasar Sudan ke hannun Masar, kome ba tafiya ya ke sosai yadda ya kamata ba. Amma kome bacin mulkin Masar, ya fi na Mahadawa sau dari. A lokacin da Mahadi ke da rai, Halifa Abdullahi bai saki jikinsa sosai da sosai ba. Sai dai kada a manta ko a lokacin nan shi ne silan duk miyagun ayyukan da Mahadi ya yi. To, yanzu fa da ya sami rana, sai ya baza shanyarsa sosai. Kusan in ce abu uku su ne karfin mulkinsa a takaice, watau zalunci, kisa da kurkuku. Duk wanda ya ke jin haushinsa, ko tsoronsa, ko kishin arzikinsa, zai gamu da daya daga cikin wadannan. Maganar adalci am bar ta tuni, alkalai sai hukuncin da aka zabam musu su ke zartarwa, ba abin da shari'a ta ce ba. Tun zamanin Mahadi am fasa makarantun addini da na ilmi, an tara littattafan shari’ar Islama duka an kona. Am fito da wata hanyar shari'a dabam wadda ba ta dogara ga Alkur’ani ba, ba ta dogara ga Hadisi ba, sai ga zalunci da biyan munayar zuciya kurum. Wannan ya sa abubuwan nan biyu suka lalace a Sudan, watau addini da shari’a.
Wajen fuskar ciniki kuma, kowa ya sani ciniki ba ya rayuwa sai da kakkarfan mulki mai adalci. Tun da ya ke ’yan kasa ma hukuma tana washe dukiyarsu, ina ya baki wadanda da ma ba su da mataimaki sai hukumar kasa ? Sabo da haka duk hajar da aka saba shigowa da ita daga Masar, daga Turai, ko daga kasashen gabas, yanzu babu damar shigarta.
Ciniki daya kadai ya ke rayuwa, shi ne bakin cinikin nan na bayi. Im fa mutum ya zagaya kasuwar bayi, zai gan su bargaja, maza da mata, yara da manya. Kila a cikin mulkin Halifa babu wadanda suka ji dadi kamar dillalan bayi, in dai ba waziransa da alkalansa ba ne. Dillalan nan, kullum ranar duniya za su sami kudi ta wajen Ia’ada da kura. Babban abin kunya game da wannan ciniki, shi ne yadda ka san a ke cinikin dabba, haka a ke yinsa, tumbana dai in an zo sayen baiwa mace, wadda za a mayar kwarkwara. Babu abin da ba a dubawa a jikinta. Ka ga am bude bakinta an duba hakoranta. A sa ta cire kallabi a duba gashin kanta, a ce ta kware riga a duba kirjinta, a duba gadon bayanta. A kewaya ta a ga siffofinta, da direwa tata. Sai kuma a ce ta yi ’yar tafiya a ga irin takawarta. Kai, babu dai abin da ba a yi wajen kalailaice halittarta. Wadansu abubuwan ma bai kamata baki ya fade su ba, balle alkalami ya rubuta.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada