ABDULKADIR SALADIN 22

22. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Ko wane maratayi ka duba, sai ka ga mutum uku ko hudu ko biyar suna lilo. Daga kasa ga haunawa sun zage dantse suna fillar kai, kamar ana fille dawa. A waje daya ga masu yanke hannu da kafa, su kuma suna dadara wuka kamar masu yankar doya. Kai, kafin lokaci kadan dai babu abin da ya rufe wurin, daga gawa sai guragun tilas. Amma ko wanne cikin mutanen nan da aka kashe, ya yi mutuwar jaruntaka. Ko kadan ba su nuna karayar zuci ba. Wadansu ma don karfin rai, kafin takobi ya sauka a wuyansu, har su kan yi wa kansu kirari. Su kan dubi ’yan kallo su ce, “Wanda bai taba ganin mutuwar jarumi ba, ya dubo nan.” Suna rufe baki sai a gutsure kan. Bayan an kare kaf, Halifa ya nufi gida, muna biye da shi. Duk cikimmu, im ba shi ba, kila ba mai sauran laka a jikinsa, sai ko haunawansa masu mummunar sana’a, ta cire kan mutane. Su kam ba su kula ba.
NA SAMI LABARIN GIDA
Bayan watanni sai wadansu fatake suka zo mini da labari, wai amsar wasikar da na yi gida ta dawo. Suka ce wai har da akwatunan kudi guda biyu. Wata rana ina zaune a kofar Halifa, sai ga wani mutum janye da rakumi. A bisa kan rakumin ga akwatunan nan biyu. Ya ce yana son ganin Halifa. Na ce daga ina ya ke ? Ya ce daga Suakin, Usman Dinga ya aiko shi.
Da aka shaida wa Halifa, sai ya ce a tafi da akwatunan baitulmali, takardu kuwa a ba magatakardansa na babban ofis. Zuciyata ta fara dar dar, na yi zaton azzalumi zai yi halinsa. Da maraice sai Halifa ya kira ni, na ga ya mika mini takarduna kurum. Da na je waje guda na bude, na ga yadda ’yanuwana suka yi murna da samun labarina daga gare ni. Suka ce yanzu hankalinsu ya dan kwanta don sun san inda na ke, sun kuma san irin halin da na ke ciki. Daya daga cikin takardun sun rubuto wa Halifa ne da larabci. Wani shaihi wai shi Wahrmund a Turai, wanda ya ji larabcin gaske, shi ya rubuta musu ita. Ya kaikaita alkalaminsa ya shiga zuba wa Halifa yabo.
Na dauki takardar sai wurin Halifa, na fadi na yi gaisuwa, na fada masa abin da tawa wasikar ta ce, na kuma mika masa tasa. Ya karanta, ya sake karantawa, don dadinta sai da ya karanta sau uku. Da yabo ya ratsa shi sai ya ce a karanta ta da karfi a masallaci, don kowa ya ji. Nufinsa ya nuna wa jama’ a watau ba a Sudan kadai ba, har Kasar Turai sunansa ya kai, adalcinsa ya kai! Sa’an nan ya ce im fada masa abin da tawa ta ce, na gaya masa. Na ce 'yanuwana sun ce in kara yi musu gaisuwa da godiyar dawainiya, da rungumar da ya yi mini. Amma don su nuna matukar godiyarsu, ga jaka nan ta fata sun ce a kawo masa, gaisuwarsu ke nan. Ya yi murna da jin haka, ya ce gobe in kawo jakar da safe. Don jin dadin takardun nan da alherin nan, har ya ba da odar a fito da akwatunan kudin nan daga baitulmali a ba ni abina, domin zuwansu yau wata da watanni bai ba ni ba.
Da na bude akwatunan na kidaya kudi, na cim ma £200 daidai. Bayan haka ga agogan hannu goma sha biyu, ga reza ta aski, ga madubi, ga jaridun kasarmu, ga Alkur'ani da aka juye da harshen jamusanci. Abin da na fara yi bayan na karbi kayan nan, shi ne karanta Jaridu. Ko wacce sai da na karance ta kaf, na ji labarin kasarmu ta Austria, da sauran kasashen Turai, da labarin duniya duka. Ko da ya ke labaran sun dan tsufa, amma a gare ni da na yi shekara shida ba ni da labarin duniya, duniya ba ta da labarina, ina ganinsu kamar yau aka buga su. Na yi watanni ba ni da abokan hira da dare bayan na komo daga aikin barantaka a gidan Halifa, sai su. Tsohon Limamin Kirista Father Ohrwalder wanda mu ke tsare tare, shi ma har ya kan biyo dare a boye ya ari wadansu ya je ya karanta.
Na kwashe kayan nan kaf sai fada, na je na baza a gaban Halifa. Da ya ga ’yan abubuwa masu kyalkyali kamar su reza, su almakashi, su buroshi, da ’yan fararen kwalabe, sai ya yi mamaki. Ya ce im bayyana masa amfaninsu da dai dai. Nan da nan kuma ya sa aka kirawo alkalai da majalisunsa, aka kewaye ni ana kallo. In na fadi amfanin abu guda, sai su nuna matukar mamaki, suna kada kai. Na san wannan fadanci ne kawai, domin na tabbata da dama cikinsu sun sha ganin wadansu daga cikin abubuwan nan. Nuna mamakinsu kurum don sun ga Halifa yana mamaki ne, sabo da haka ba su da iko su nuna sun san su.
Da aka gama ya ce wa daya daga cikin magatakardunsa ya rubuta amsa da larabci zuwa ga ’yan uwana. Ya fada musu godiyar Halifa sabo da samun wasikarsu da kuma alherin da suka aiko masa. Danuwansu kuwa, Abdulkadir, yana nan cikin ni’ima da karuwar daraja a kullum. Kuma yana so su zo Omdurman su bakunce shi, bayan kwana biyu su koma gida. Ni kuma aka ba ni iznin in rubuta musu amsa. A ciki na gargade su, na ce ko da mafarki kada su ce za su zo Omdurman. In sun zo fa sun zo kenan, da su da kubuta su koma Turai sai kwaton Allah. Aka jefa wasiku a ambulon aka like, aka ba manzo ya nufi Suakin.
Ran nan ina cikin zamana, sai kuma na sake fadawa cikin wani hadarin. Aikin dai ke nan, yau in na fita wannan tarko, gobe a kafa mini wani. Yadda wannan ya faru kuwa, wai wani ne ya zo daga Masar, ya tsegunta wa Halifa, cewa wai ni dan rahoton gwamnatin Masar ne. Ina zaune a zauren kofar gida tare da 'yanuwana barori, ’yan iso, sai aka ce in shiga Halifa na kira. Gabana ya yi ras ya fadi, na dai kanne na shiga. Na same shi zaune, majalisa ta cika. Na fadi na yi gaisuwa, na sunkuyad da kaina kasa.
Ko da ya bude baki, bai ce mini shai’an ba, sai ya shiga magana da majalisarsa. Ya ce musu, “Tun ran da Abdulkadir ya shiga hannummu na ke fada masa zuciyarsa ta bar rudinsa. Ba shi da abin yi illa ya ba da gaskiya gare mu daga baka har zuci, amma bai yarda ba. Na dauki Abdulkadir kamar dana na cikina ne, amma shi kullum tsakaninsa da ni sai dungu.” Ya juyo kuma gare ni ya ce, “Abdulkadir, mu Larabawa a karin maganarmu mu kan ce, “Duk inda ka ga hayaki, da wuta a wurin.” Naka hayakin kuwa ya yi yawa har ya murtuke. Manzo ya zo mana nan jiya daga Masar, ya ce kai dan rahoton hukumar Masar ne. Masar tana aiko maka da albashi ladan aikin da ka ke mata na rahoto, har ya ga baucar da ka sa hannu a ofishin wakilin kasarku ta Austria, wanda ke Masar. Ya ce kun yi kulli da hukumar Masar za ka koma bayansu in sun kawo mana yaki, har ma za ka nuna musu taskokimmu na harsashi. Wannan zance kuwa yana da kanshin gaskiya tun da ya ke taskar harsashi a kusa da gidanka ta ke. Amma duk da haka, sabo da amincewa da na yi da kai a zuciyata, ban gaskata mai ba da wannan labari ba, har na kama shi na daure. To, amma ko kana da hujjar munafuntarmu har ka rika kai rahotommu, bayan mun jawo ka a jikimmu haka ?"
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)