24. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Ciniki daya kadai ya ke rayuwa, shi ne bakin cinikin nan na bayi. Im fa mutum ya zagaya kasuwar bayi, zai gan su bargaja, maza da mata, yara da manya. Kila a cikin mulkin Halifa babu wadanda suka ji dadi kamar dillalan bayi, in dai ba waziransa da alkalansa ba ne. Dillalan nan, kullum ranar duniya za su sami kudi ta wajen Ia’ada da kura. Babban abin kunya game da wannan ciniki, shi ne yadda ka san a ke cinikin dabba, haka a ke yinsa, tumbana dai in an zo sayen baiwa mace, wadda za a mayar kwarkwara. Babu abin da ba a dubawa a jikinta. Ka ga am bude bakinta an duba hakoranta. A sa ta cire kallabi a duba gashin kanta, a ce ta kware riga a duba kirjinta, a duba gadon bayanta. A kewaya ta a ga siffofinta, da direwa tata. Sai kuma a ce ta yi ’yar tafiya a ga irin takawarta. Kai, babu dai abin da ba a yi wajen kalailaice halittarta. Wadansu abubuwan ma bai kamata baki ya fade su ba, balle alkalami ya rubuta.
Wajen fuskar sana’o’i da noma kuma yadda kome ya mutu, haka suka mutu. Sana’a guda kadai ke da dan rai, ita ce kira.Dalilin wannan kuwa ba a boya ya ke ba, don kera makamai ne sabo da sojan Halifa.
Bai kamata in kare bayanin mulkin Halifa, ba tare da bayanin kurkukun Birnin Omdurman ba. Kullum safiya za ka ji an jefa Wane yau a kurkuku, an kashe Wane yau. Kurkukun wani katon gida ne gabas maso kudu da gari, kusa da Kogin Nil. Shiga ciki ka ga abin tausayin da zai sa kwalla ta faso maka! Dakin da fursunan ke kwana, ko da rana ka shiga ba ka iya ganin tafinka, sabo da duhu. Ba taga, ba dabe, ba tabarma, sai bisa busasshen ingirici su ke kwanciya. Galibinsu nauyin sarkar da ke kafafunsu da wuyansu, ya fi nauyin jikinsu. Abinci tafin hatsi guda a ke ba su, shi ne kalaci, shi ne abincin rana, shi ne na dare. Kuma tsukunsa su ke yi danye, sai yawun bakinsu, sai ruwa.
Ko da ya ke ni kaina na sha dauri kamar dame, an daure ni da sarka a kafa, a gindi, a wuya, amma ba na manta irin azabar da wadansu suka sha. Ba na mancewa da Charles Nenfeld, wani Bature da Halifa ya jefa a kurkuku, ya yi shekaru ana gwada masa matukar azaba. Wata rana azabar ta kai matuka, har ta sa ya ture, ya ki shig a daki. Sabo da haka durobobin kurkukun nan suka kewaye shi, suka yi ta bugun sa da dorina, amma bai motsa ba, bai kuma ce uffan ba, har suka gaji da duka suka bar shi. Abin da ya sami Charles Nenfeld, shi ya sami Shaihu Halil, da wahi Bayahude wai shi Malech, har da Asakir Abu Kalam, wanda shi ya taimaki uban Halifa da abinci da sutura, lokacin da su ke talauci.
Amma duk wadanda suka fi kowa ganin tasku, su na Zeki Tummal da Kadi Ahmed, wani babban masoyin Halifa a da. Su, maimakon a jefa su cikin sarka, sai aka gina wani dan daki dogo, mai kamar bututu. Babu kofa, sai daga sama a ke sako mutum, kamar an jefa dami cikin rumbu. Daga ciki, babu yadda mutum zai zauna sabo da kunci, a tsaye zai tsaya dare da rana, an sa murfi an rufe saman. In gari ya waye sai a taka tsani a bude murfin a zuraro musu tafin dawa, da makwarwar ruwa daya. In sun ci, sun sha, a rufe. Cikin dai kwana kadan azaba ta ci karfinsu, suka mutu a tsaye, don babu yadda gawar za ta fadi. Aka jawo su aka kai makabarta a bayan gari, aka yi musu karbi-a-jika, ba wanka, ba salla. Don karin wulakanci, har wa yau, Halifa ya ce in za a saka su a kabari, a juya fuskarsu yamma ne, su tura wa Makka baya. Musulmi kuwa, duka wajen Makka a ke sa fuskarsa, in an kwantad da shi a kabarinsa.
NA SHIGA DABARUN TSEREWA
Ina nan ina barantaka a gidan Halifa Abdullahi. Ran nan sai aka kafa mini wani sabon aiki. Shi Halifa mai son agogai ne, kuma yana da su da yawa. Sai aka sa su a hannuna. Ni ne mai goge su, da ba su waini a kullum. A cikin Omdurman akwai wani Bature wai shi Artin, sana’arsa ke nan gyaran agogo. Yana zaune a unguwar Turawa, watau ’yan Turawan da ba su sami tserewa ba, a lokacin da Mahadi ya ci Sudan. Wadansu ’yan kasuwa ne a da, wadansu kuwa aikin mishan su ke yi, wadansu na gwamnati. Amma yanzu duk kowa ya kama sana’ar hannu ta neman abinci. To, in ina so in debe kewa, can unguwar tasu na kan je in ji labarin duniya, tun da ya ke su suna saduwa da fatake, masu zuwa daga Suakin, a bakin Bahar Maliya. Amma ba su da ikon barin garin, ko dare ko rana, balle su tsere. Hujjar da na kan bayar, na kan ce zan tafi in kai wa Artin agogo ne ya gyara, ta haka sai Halifa ya yarda.
'Yanuwa da abokai a Alkahira, a Masar, sun san ba shi yiwuwa su samo mini 'yancina a wurin Halifa. Saboda haka suka shiga dibarbarun yadda za su samo mini hanyar tserewa. Ni kaina tun ran da aka kama ni, na san ba ni da wata hanyar kubuta, sai ta tserewa kurum. Kuma ko da ya ke wannan tsarewa da aka yi mini a Sudan ta amfane ni a wani hali, duk da haka kome dadin bauta ’yanci ya fi ta. Balle ni ma irin tawa bautar ba ta da dadi ko ko kadan. Amma duk shekarun nan ban taba hurta wa wani mahaluki irin niyyata ba, sai Ibrahim Adlan kadai. Shi kadai ne na yarda da shi fiye da kowa, har Turawa ’yanuwana, su Artin. Amma ba a dade ba sai zaluncin Halifa ya bi ta kansa, aka rataye shi. Na zauna ba ni da kowa amintaccena.
Ran nan cikin watan Fabrairu, 1892, sai ga wani Balaraben Assuan wai shi Bubakar Abu Sebiba. Ya zo fada ya ce ya kutto ne daga mulkin Masar don ya yi caffa ga Halifa. Ashe shi ne manzon alheri gare ni! Halifa ya karbi caffarsa, ya shafa kansa a masallaci, ya sa masa albarka. Ana tashi daga masallaci, kafin Halifa ya motsa mu bi shi zuwa gida, sai mutumin nan ya goge ni, ya ce mini cikin rada, “Dominka na zo nan kasar. Fada mini inda za mu sadu.” Na yi maza na ce masa gobe, bayan sallar azahar, a nan masallaci. Ya wuce, na wuce.
Gobe na yi, duk na kosa azahar ta yi. Ko da ta yi muka je masallaci, sai ga Bubakar. Ya faki idon mutane, muka shige wata ’yar bukka a harabar masallaci, ya sunna mini wani dan karamin akwatin karfe da ganyen ti a ciki, ya ce, “Wannan akwatin gindinsa biyu ne, in ka bude na can kasa za ka tarad da takarda. Kome ke akwai kuma za ka gani, im mun sadu gobe ma shirya abin da za mu yi.” Na sulle akwatin nan da kyau a cikin jabbata, don yana warin ganyen ti. Abun mamaki, muna isowa fada, sai Halifa ya yi minu abin da ya yi shekaru rabonsa da ya yi mini. Ya ce in zo mu ci abinci tare. Wayyo Allah, malam kada ka so ka ji yadda gabana ke faduwa, dar dar dar, da jin haka! Dalili kuwa, na tabbata im bai ga tudun akwatin nan a cikin rigata ba, zai ji kanshin ganyan ti yana fitowa daga jikina. Amma duk Ubangiji cikin rahamarsa ya kyauta, babu dayan da ya faru.
Muna kare cin abinci sai na yi karyar ciwo, na ce ina so in tafi gida. Halifa ya ce in je in kwanta. Don doki har tuntube na ke yi a hanya, duk na kosa in ga abin da ke cikin takardan nan ta akwatin ti. Ina zuwa na rufe kofa, na kunna fitila, na jawo takardar. Ko da na buda, sai na ga rubutu layi daya kurum, an ce, “Bubakar Abu Sebiba yardajje ne.” Mai sa hannu Kanar Schaeffer. A daya shafin kuwa ga ’yan shedaru da wakilin Austria na Masar ya rubuta don tabbatad da gaskiyar Bubakar. Kashegari muka sake haduwa da Bubakar a masallaci. Muka kebe, ya fada mini da rada, ya ce an aiko shi ne don ya taimake ni in kubuta. Ya ce amma in yi hakuri sai watan Yuli, yanzu shi zai koma Berber, ya ci gaba da shiri. Muna cikin Fabrairu ne, sabo da haka na yi ta jira har Yuli ya kama. Wata ya kai kwana goma ban ga Bubakar ba, ya raba, ban ga Bubakar ba, ya kai ashirin, kai har dai ya kare ba Bubakar.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com
http://bukarmada.wordpress.com
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada