AKUSHIN MATA TUBALI

*AKUSHIN MATA TUBALI*

02-10-2018


Tareda: *UMMU ALEESHA WA WALEED*




*Wainar semovita*




1-semovita Leda daya

2-baking powder

3-yest

4-sugat

5-ruwa




Dafarko zaki samu semovita dinki ke juye ta acikin roba babba ko kwano sai ke zuba baking powder dinki babban cokali guda uku sai ke kawo yest dinki shima babban cokali guda uku sai ke kawo sugar dinki ke zuba kamar gongoni daya da rabi na awo acikin sai ke kawo ruwa ke zuba ke jiya sosai kamar yadda zaki zuba ruwan talgen ke da Dan kauri kadan idan kina gama juyawa sai ke samu murfi ke rufe shi ke dauka ke ajiye shi acikin rana sai kina yi kina dubawa har sai kinga ya tashi sai ke dauko shi ke kawo kitchen ke ajiye shi nan kuma ga kaskon suyar wainar ke kin daura akan wuta sai ke jiya wannan kulin sosai SBD ya saki jikin shi idan kika kikaga yayi miki kaure sosai sai ke zuba ruwan kadan acikin ke kara juyawa idan kina gama nan kuma ha kaskon ke kin zuba mai acikin idan mai yayi zafi sai ke fara zuba kullin ke aciki kina soyawa kamar yadda zaki yi wainar shinkafa ana cin shi da miyar taushi ko kuma ta agushi .


*MATA TUBALIN AL'UMMA*




*Daga Akushin mata tubali🍝*


🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲


*AKUSHIN MATA TUBALI*




Tareda: *UMMU ALEESHA WA WALEED*




*Zobo drink*


Zobo danye
Citta
Kanunfari
Cucumber
Na'a Na'a
Flavor
Sugar



Dafarko zaki zuba zobon ke acikin tukunya sai ke dauraye shi da ruwa bayan ke dauraye sai ke kawo ruwa ke zuba acikin dai-dai misali amma ya hauro kan zobo sai ke kawo kanwar ke ki zuba acikin saboda tsamin shi ya ragu sai ke zuba cittar ke da kuma kanunfarin ke acikin ke daura akan wuta bayan ya tafasa sai ke sauke shi sannan ke dauko na'a-na'ar ke danya ko busasshiya ke zuba acikin sai ke rufe tukunyar ke bata Dan mintina kadan bayan kin bata Dan mintuna sai ke taci zubon nake nan kuma ga cucumber dinki wadda kina markadata acikin blender itama sai ke taci ta sai ke kawo ruwan nata ke zuba acikin zobon idan kina kina so ki rings cin ta acikin zobon sai ke rabata biyu tun kafin ke markada sai ke yanka rabi kiyi mata yankan sliced rabi kuma sai ke markada shi bayan kin gama hadawa sai ke kawo flavour dinki da sugar ke zuba acikin idan ya juye sosai sai ke saka a fridge Dan yayi sanyi asha dadi lfy.




*MATA TUBALIN AL'UMMA*



*Daga Akushin mata tubali🍝*


🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲


*AKUSHIN MATA TUBALI*




Tareda: *UMMU ALEESHA WA WALEED*




*Farfesun kifi mai daddawa*




1-kifi(ko wani iri)

2-tumatur na Leda

3-attaruhu

4-albasa

5-daddawa

6-maggi,gishiri,tafarnuwa

7-mangayda,masoro





Dafarko zaki samu kifin ke ko wani iri na ke wanke shi sai ke ajiye shu gefe guda nan kuma ga attaruhun ke dai-dai yadda kike so kin jajjaga shi sai ke kawo albasar ki mai Dan yasa ki yankata kananu itama sai ke samu tafarnuwar ke da masoro ki jajjaga su tare sai ke samu daddawar ke dai-dai misali ke daka ta itama ke ajiye,bayan duk kin gama hada kayin aikin ke sai ke dauko tukunyar ke ki zuba mata mai acikin sai ke kawo attaruhun ke da tumaturun Leda ke zuba acikin idan yadan soyu kadan sai ke samu ruwa ke zuba acikin dai-dai misali sannan sai ke kawo daddawar ke itama ke zuba acikin sai ke rufe tukunyar amma zaki Dan bude kadan saboda Gafin daddawar ya ringa fita daga ciki idan ruwan ya tafasa sai ke kawo kifin nan nake ke zuba acikin sai ke kawo albasa da tafarnuwar nan mai masoro tare dasu maggin ke da gishiri duka sai ke juya ya had I jikin shi sannan sai ke rufe tukunyar take amma zaki ringayi kina dubawa har ya dahu shikenan kin gama farfesun ke.




*MATA TUBALIN AL'UMMA*




*Daga Akushin mata tubali🍝*


🍲🍲🍲🍲🍲🍲


*AKUSHIN MATA TUBALI*



Tareda: *UMMU ALEESHA WA WALEED*



*Local salad*



1-salad

2-albasa

3-dankalin Hausa

4-tumatur,koren tattasai

5-cucumber

6-vinegar

7-oil,maggi

8-kwai




Dafarko zaki tanka salad dinki ke wanke shi vinegar sai ke ajiye shi gefe guda sannan ke samu tumatur dinki da cucumber suma ke yanka su shima dankalin hausar ke zaki dafashe na ke yanka shi kananu kwai shima ke yanka shi kananu idan kina gama hada wadan nan abubuwan nake sai ke ajiye su gefe guda sannan sai ke samu albasar ke wadda kina yanka ta kananu itama amma da Dan yawa kadan sai ke daura kaskon ke akan wuta ki zuba mai kadan sai ke samu albasar nan ke juye ta acikin sai ke kawo vinegar dinke ke zuba kamar murfi biyu na roba sai keyi ta juyawa zakiga albasar ke tayi laushi kuma tayi colour mai kyau idan kika gama sai ke dauko salad dinki ke zuba shi cikin babbar container sai ke kawo duk abubuwan nan da kika yanka me zuba acikin sannan sai ke kawo albasar da kika soya mai vinegar itama ke zuba acikin sai ke samu mai ke zuba acikin amma kadan sannan ke zuba maggi shima sai ke juya shi ya juye sosai da sosai komai ya shiga jikin juna shikenan kin gama local salad dinki ana cin shi haka koda shinkafa da wake ko kuma shinkafa da miya.




*MATA TUBALIN AL'UMMA*



*Daga Akushin mata tubali🍝*

🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲

*AKUSHIN MATA TUBALI*


tareda: *UMMU ALEESHA WA WALEED*



*Meat roll*


1-flour 2cups

2-teaspoon of sugar 2

3-milk 1teaspoon

4-baking powder 1teaspoon

5-butter 2 tablespoon



Zaki hada flour dinki da kayan hadin nan gaba daya sai ke juya su sosai koma ya shiga bayan kin gama sai ke kawo ruwan ke ki zuba shi acikin ke kwaba sa sosai amma kar yayi ruwa sosai kuma kar yayi kauri kamar kwabin cin-cin idan kin gama kwabawa sai ke samu chopping bord dinki ke daura shi akai ke Mirza shi da fada sosai da sosai idan yayi dadi sai ke kawo hadin naman ke Wanda kina dafa shi kuma kika soya da attarhu dasu maggi sai ke zuba akan wannan flour din da kikace fadada din sai ke fara nade ta Kamar yadda zaki nade tabarma haka zaki yi mata har ki gama idan kina gama sai ke samu wukar ke ke yanka wannan flour din da kikace nade din into pieces kamar hudu sai ke kunna oven dinki ka shafa butter dinki akan pan din oven din sai ke kawo meat roll dinki ke daura akai sai ke kunna oven din kiyi baking din shi idan yayi sai ke sauke anfi yin shi da safe saboda breakfast.




*MATA TUBALIN AL'UMMA*



*Daga Akushin mata tubali🍝*


Post a Comment (0)