ME YASA CAKE YAKE TAURI?

Ok

1-MEYASA SAKA CAKE YAKE TAURI?

Mostly abinda yasaka cake yakeyin tauri shine cika flour kuma a saka ingredients din kadan misali zakiga mace zatayi cake na Rabin kwano sekiga ta saka kwai biyar one simas ko man kuli kuli kuma duk sekiga ta gwamutsatsu ta mitsitstsekesu ta gasa batare da tabi abun step by step ba kinga kuwa ai dole a dinga samun matsala.

2- MEYAKE SAKA CAKE YAKE BUSHEWA?

Mafi akasarin abinda yasaka cake yake bushewa shine barinsa a sarari iska tana kadawa koina kokuma sakashi a fridge ba tare da kin rufe da wani abunba kinga kuwa kafin lkci kalili sekiga ya bushe kokuma saka butter kadan bayan kinsan yana bukatar butter.

So,idan kinason cake dinki yayi laushi seki tanadi kwai ishashshe butter da kuma baking powder daidai gwargwado.idan kinason cake dinki yadena bushewa seki tsaya ki duba flour Kofi nawa kika saka kuma kayan hadin yaya yakamata ki sakasu ,bayan kin fiddashi daga abin gasawa idan ya huce seki samu roba me murfi kixuba ki rufe kokuma kisamu Leda kiyi kulli ba lallai sekin saka a fridge bama.

3-MEYAKE SAKA CAKE YAKE RASHIN DADI?.

Abinda yasaka shine rashin saka abinda aka cemiki kokuma cika abinda akace miki kokuma rage abinda akace miki,misali idan akace miki baking powder cokali 2 sekika saka 3 kinga taste din cake dinki dole ya canxa kokuma yakiyin dadi,kokuma ace miki sugar 1 cup sekisaka 3 kinga cake dinki bazeyi dadi kokuma kicika butter kinga kin lalata cake dinki .

Bin ka'ida yadda akace miki Abu ba tare da kinyi ragi ko kariba ze taimaka miki sosai wajen yin dadin cake dinki( misali yanxu idan kika cika madara zakiji yayi dadi Kamar madara ,idan kika cika kwai zeyi karni,idan kika cika butter zeki tashi,idan kika cika baking powder ze canxa taste etc)


4-MEYAKE SAKA CAKE YAKE KIN TASHI?

Shine rashin saka baking powder me kyau idan kika saka masa baking powder Mara kyau toh insha Allah baze tashiba kokuma kika cika masa butter shima haka,yakamata a dinga kiyayewa.
Post a Comment (0)