CIYAR DA MATAR MARA ƘARFI


*CIYAR DA MATAR MARA KARFI:* 

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

*TAMBAYA*❓

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Idan mutum ya aurar da ’yarsa ga mara ƙarfi, to wai ciyar da ita ya koma kan mahaifinta kuma?

*AMSA*👇

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] A asali nauyin ciyar da mace watau: Ɗaukar nauyinta ta fuskar abinci da tufafi da magani da kuɗaɗen makaranta da sauransu muhimman buƙatunta a rayuwa, suna kan mahaifinta ne kafin aurenta. Allaah ya ce:

 ۞ وَٱلۡوَ ٰ⁠لِدَ ٰ⁠تُ یُرۡضِعۡنَ أَوۡلَـٰدَهُنَّ حَوۡلَیۡنِ كَامِلَیۡنِۖ لِمَنۡ أَرَادَ أَن یُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَۚ وَعَلَى ٱلۡمَوۡلُودِ لَهُۥ رِزۡقُهُنَّ وَكِسۡوَتُهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ
Kuma uwaye suna shayar da ’ya’yansu na tsawon shekaru biyu cikakku ga wanda ke son ya cika shayarwar. Kuma wajibi a kan wanda aka haifa masa ya ciyar da su, ya tufatas da su yadda aka sani. Ba a ɗora wa wani rai face dai iyawarsa. (Surah Al-Baqarah: 233).

Kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fada wa Hindu matar Abu-Sufyaan (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:

« خُذِى مَا يَكْفِيكِ وَوَلَدَكِ بِالْمَعْرُوفِ »
Ki ɗebi abin da zai wadace ki da ’ya’yanki yadda aka sani.

[2] A bayan tarewarta kuma ciyarwar mace ya koma kan mijinta ne, kamar yadda Ubangiji Ta’aala ya ce:
لِیُنفِقۡ ذُو سَعَةࣲ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَیۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡیُنفِقۡ مِمَّاۤ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا یُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَاۤ ءَاتَىٰهَاۚ سَیَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرࣲ یُسۡرࣰا
Ma’abucin wadata sai ya ciyar daga wadatarsa, kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa sai ya ciyar daga abin da Allaah ya ba shi. Allaah ba ya ɗora wa wani rai sai iyakan abin da ya ba shi kawai. (Surah At-Talaaq: 7)

Sannan kuma Al-Imaam Muslim (3009) ya riwaito dogon hadisin Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) inda ya siffata hajjin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), har inda yake cewa a cikin wa’azinsa ga al’umma a kan haƙƙoƙin ma’aurata:
 
« وَلَكُمْ عَلَيْهِنَّ أَنْ لاَ يُوطِئْنَ فُرُشَكُمْ أَحَدًا تَكْرَهُونَهُ. فَإِنْ فَعَلْنَ ذَلِكَ فَاضْرِبُوهُنَّ ضَرْبًا غَيْرَ مُبَرِّحٍ وَلَهُنَّ عَلَيْكُمْ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ».
Kuma yana daga cikin haƙƙinku a kansu: Kar su bayar da shimfiɗunku ga duk wanda kuke ƙyamatarsa. Idan kuwa suka aikata haka sai ku doke su dukan da ba mai tsanani ba. Su kuma suna da haƙƙin cewa: Ku ciyar da su kuma ku tufatar da su kamar yadda aka sani.

[3] Idan miji ya zama mawadaci amma kuma ya ƙi ciyar da matarsa saboda rowa ko ƙoro kawai, a nan malamai sun yarda matar ta ɗebi daidai abin da ya dace da haƙƙinta, ita da ’ya’yanta, saboda izinin da ya bayar ga Hindu:

« خُذِى مَا يَكْفِيكِ وَوَلَدَكِ بِالْمَعْرُوفِ » 
Ki ɗebi abin da zai wadace ki da ’ya’yanki yadda aka sani.

Malamai sun yi wa wannan izinin fassarori iri biyu: 

(i) Ko dai ya bayar da shi a matsayin hukuncin alƙali ne, ta yadda mace ba za ta iya ɗiba daga dukiyar mijinta marowaci ba sai da umurnin alƙali.

(ii) Ko kuwa yana a matsayin fatawa ne, ta yadda macen tana iya ɗiban abin da ya daidai da buƙatarta ko ba tare da izinin alƙali ba.

Amma dai malamai sun yarda cewa: Ba ta da ikon ɗiba daga dukiyarsa sai a lokacin da ita kanta ta zama mace ce shiryayya natsattsa, ba wawanya ba.

[4] To, idan mijin ya kasa ciyar da ita saboda talauci ko dai wata larura makamanciyar haka, malamai sun sha bamban a kan haka. Wasu malamai sun zaɓi cewa wajibi ne a raba auren, ta koma gidan iyayenta kawai! Tun da dai akwai cutarwa ga cigaba da zamanta tare da shi a haka. Kuma Allaah ya ce:

 وَلَا تُمۡسِكُوهُنَّ ضِرَارࣰا لِّتَعۡتَدُوا۟ۚ
Kuma kar ku riƙe su a bisa cutarwa domin ku kai ga ƙetare haddi. (Surah Al-Baqarah: 231)

[5] Amma wasu malaman ba su goyi bayan wannan shawarar ba. Sun zaɓi cewa maimakon a raba auren gara dai a bar ta tare da mijin, amma iyaye da sauran dangi su cigaba da taimakawa da abin ɗaukar nauyin ciyarwar. Tun da a iya tsawon rayuwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba a taɓa jin inda ya raba auren wata mace saboda talaucin mijinta ba! Ban da ma wadda ya ɗaura mata aure da mijin da ba shi da komai! Sannan kuma a lokacin da matansa suka nemi ƙarin ciyarwa sai kowanne daga cikin manyan sahabbansa: Abubakar da Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) suka yi wa ’ya’yansu faɗa, har kuma suka horar da su a kan hakan. Amma kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai hana su ba. A ƙarshe kuma har Allaah ya saukar da:

یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّبِیُّ قُل لِّأَزۡوَ ٰ⁠جِكَ إِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱلۡحَیَوٰةَ ٱلدُّنۡیَا وَزِینَتَهَا فَتَعَالَیۡنَ أُمَتِّعۡكُنَّ وَأُسَرِّحۡكُنَّ سَرَاحࣰا جَمِیلࣰا

وَإِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلدَّارَ ٱلۡـَٔاخِرَةَ فَإِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡمُحۡسِنَـٰتِ مِنكُنَّ أَجۡرًا عَظِیمࣰا
Ya kai Annabi! Ka gaya wa matan aurenka: Idan kun kasance rayuwar duniya ce kuke nufi da kayan kwalliyarta, to ku zo in jiyar da ku daɗi kuma in sake ku saki mai kyau. Idan kuma kun kasance Allaah da Manzonsa ne kuke nufi da kuma gidan Lahira, to haƙiƙa Allaah ya yi wa mai kyautatawa daga cikinku tattalin lada mai girma. (Surah Al-Ahzaab: 28-29)

Kuma ba tare da sun yi shawara ko da iyayensu ba, sai dukkan matan suka zaɓi Allaah da Manzonsa da Gidan Lahira. Ga ƙissar nan a cikin Sahih Muslim (3763).

Idan kuma an rasa waɗanda za su iya ɗaukar nauyin hakan daga cikin dangi da ’yan uwa, sai nauyin ciyarwar ya koma kan al’ummar musulmi, daga cikin baitul-maali.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)