TUN KAFIN AURE 18

TUN KAFIN AURE💐 18
Hakika mutuwa abin tsoro ce musamman ga irinmu masu aikata sabo muna sane. Kamar yadda na fada a gidanka Alhaji waazi naji yayi matukar razana ni. Ina tsoron mulki yanzu, ina tsoron kudi, ina tsoron haduwa da Allah akan laifukana sannan ina tsoron samun kamasho daga laifukan Junaid tunda laifina ne abinda yake yi. Akan yarinyar nan ya dawo gida da guduwa yayi. Akan ta yayi min alkawarin shiryuwa shiyasa kaga na dage. Idan har na mutu yana wanan rayuwar kabari zai min kunci. Kuka ne yaci karfin senator sai dai su uku mazan akwai hawaye a idanunsu. A wannan zamani hanyoyin dulmiyar da bayin Allah akwai yawa ga bayyana sabo saboda rashin tsoro. Mal Aminu yace zan amince amma sai anyi masa gwaje gwajen cutuka saboda lafiyar Hafsa. Ko sau daya kada yazo gidana sai na tabbatar da lafiyarsa sannan zaa fara maganar aure. Abu na karshe zamu rubuta yarjejeniya kai Alhaji ka zama shaida duk ranar da ya koma ga miyagun halayensa bayan aurensu kun amince kotu ta raba auren idan yaki shiryuwa. Na yarda na amince kawai senator yake fada. Ba zai iya fada musu mugun mafarkin da yayi yaga kansa cikin wuta yana ta shan azaba ba a dalilin dukiyar da suke wadaka da ita. Abin tamkar gaske ya gani. Mutuwar abokinsa washegarin mafarkin wani wanda yayi gwamna karo biyu sun shiga sun fita ya zama minista shi ya kara tada masa hankali. Gawar abokin nasa bakikkirin kamar an shafa gawayi gashi yaransa suna ta murna harda party ranar da yayi bakwai wai giwa ta fadi. Sosai ya tsorata har baya iya baccin kirki. Uwa uba kuma yaga yadda hukumar kama masu watanda da arzikin kasa su cinye a cikinsu tasa mutane a gaba. Wannan tonon asirin ma na duniya ya ishi bawa mai tsoron Allah.
*******************
Kuka take sosai a daki tunda Baffa ya sanar da ita abinda ke faruwa. Duk gidan al'amarin bai musu dadi ba Mama tana ta mita. Hafsi tayi fushi sosai da Saif da ace wani abu ma ya faru tsakaninsu haka zai fasa auren karshe duk wanda ta aura yaci mata zarafi. Yanzu duk farincikin da take baffa ya yafe mata ashe hoton nan bazai fasa jawo mata sabbin masifu ba kullum.
Ummati ce ta shigo da sallamarta Hafsi ni fa ban gane zancenki ba a waya. Rungume aminiyarta tayi tana kuka tana sake mata bayani. Ummati ta kalleta yanzu shi dan sanatan kin ganshi? Ke wa yake ta tashi ko sunansa ma ban sani ba. Ai kinji dadi Lawal baizo kun yi naku hotunan ba. Wannan hoto bai zo min da komai ba sai sharri. Ummati rarrashinta kawai take tana tuna yadda Allah Yasa ta auna arziki bata riga tayi hoton ba. A da suna wa abin kallon wayewa sai dai yanzu sunyi karatun ta nutsu. Duk wani hani ko umarni a musulunci akwai alkhairi mai kyau a tare da shi.
*******************
Da sassafe Junaid ya tafi asibiti. Sam daren jiya baiyi bacci ba tunda Hajiyan Dangi ta sanar dashi yadda mahaifinsa yayi dasu Baffa. Ya tabbatar ba wani abu Baffan ke tsoro ba sai HIV da sauran dangin cututtukan da ake kamuwa dasu ta wannan hanyoyin.
Batul Mamman💖


Post a Comment (0)