TUN KAFIN AURE 19

TUN KAFIN AURE💐19


Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama gano gidan da yayi masauki abinda ya rage mata yadda zata sami damar yi masa abinda bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari motar nan ta bace mana bazan biyaka ba yau...dreban taxi din ya kara gyara mirror din gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har mace sai dai babu alamun mutumci a tare da ita. Kallonta yake yana hadiyar  yawu saboda irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A bakin gate din wani asibiti yayi parking inda yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar da gayya don ta tada hankalin maza...a zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba aure ba kullum yana yawo da ita a gari.

Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi masa wanda suka hada da HIV da hepatitis. Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba kowacce mace yake muamala da ita ba kuma yana amfani da hanyoyin kariya amma dai gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane baka da wayo a hannuna.
******************

Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya nema take shiyasa suka yi shawara da ummati kan cewa bazata musa musu zancen auren dan senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa yi mata zancensa.

A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie. To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi ko hello. Harara ta galla mata  Ke ni bani abinci kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.

Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta ture plate din abincin can gefe. Tana sakace hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi ba these days amma naga baya zuwa wuraren shakatawa. Da na yanke shawarar na biya doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi tunanin kada yaje wani ya sake aga negative. Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two months kawai sai muje gidansu. Two months kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
 Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin shawara don har yau Mal Aminu bai gama sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka asirce.

Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano. Baffa kam sai da yaga result din tests har daga asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid damar yazo ganin Hafsi.
******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa yace su zauna yadda mutane zasu rinka wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa mata. Ido kawai ya bita dashi.....you are so beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana Hafsi ko....ya fada yana daga gira daya. Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can't wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin wanda black americans na ghetto suke sawa. Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko?  Firgigit ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai sai tace masa a'a. Ya zaro ido me kika ce? Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa. Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.



Batul Mamman💖


Post a Comment (0)