TUN KAFIN AURE 17

TUN KAFIN AURE💐17
Sakin baki Baffa yayi yana kallon Alh Bashir, Senator Rufai da Saif. Wane irin rainin hankali ne suka zo masa dashi. Gyara zama yayi ya kalli Alh Bashir...yanzu kana nufin ranar asabar da wani zaa daurawa Hafsa aure ba da Saifullahi ba? Wai ni Alhaji me kuke nufi da ni da iyalina ne? Akan hoton da yaron nan ya sa Hafsa taje  suka yi babu abinda banyi mata ba karshe kuma sai kawai kace min daban yana son aurenta kuma ka amince. To kai ma ka amince ne? Ya tambayi Saif. Sunkuyar da kansa yayi kasa. Shi kam kunya tasa har zuci baya son auren nan don bazai juri haduwa da mahaifinta yana tuna ranar da ya kama su a mota ba.
Zuciyarsa har neman tafasa take don a yadda yake ji a ransa ko gyada aka dora masa a kan kirji tsaf zata soyu. Ina amfanin dan cikinka ya dauko maka abin kunya. Ba don hoton nan ba sam bazai damu ba idan Saif ya fasa auren Hafsi. Senator Rufai da yake gefe yana kallon abinda ke faruwa a falon yayi dan gyaran murya don ya fuskanci kwata kwata kudinsa da mukaminsa baiyi wa Mal Aminu kwarjini ba. Kallon da ya yiwa Baffan hafsi yasa yayi shiru...malam tun a gidansu munyi magana dasu yaron yace indai ka amince to zai iya hakura da ita. To a wane dalili ne wai zaku mayar dani karamin mutum irin haka? Ko don ba 'yarka bace shine zaku rinka juya min ita kamar waina. Bakin Baffa har kumfa yake yana magana ba karamin bacin rai ya shiga ba kila kudi senator ya basu shine suke neman yi masa wannan cin kashin. Senator Rufai yayi masa bayanin halin da dansa yake ciki da tsoron karin lalacewarsa sai baffa ya kada baki yace wato lalataccen danka kake so ya shiryu sanadiyarta ko? Idan kuma abin ya faskara ya dora min ita akan turbar  lalacewa fa? Haka yayi ta fada karshe yace ni dai gaba daya na fasa bawa kowa Allah Ya hada kowa da  rabonsa.
Abin da senator yake ta kokarin boyewa game da jikinsa ne ya faru don kuwa yana tashi kirjinsa ne ya fara ciwo sai jiri ya debeshi ya fadi. Baffa ko kallonsa baiyi ba don a tunaninsa na karya ne tunda yaga kudi bai dauke masa hankali ba. Saif da Alh Bashir kuwa da sauri suka yi kansa Alh Bashir a tsorace yace haba Aminu taimaka mana. Idan mutumin nan ya mutu a gidan nan wallahi duk sai an daure mu ko a yanke mana hukuncin kisa.
*******************
Alh Bashir da Mal Aminu ne tsaye gaban gadon da aka kwantar da Senator Rufai bayan yasa iyalinsa sun dan basu wuri. Da kyar yake maģana yace nasan a dalilina kun sami sabani amma bisa amana zan fada muku sirrina. Hakika duk wata kujerar iko a kasar nan is addictive maana idan aka hau ba'a son sauka indai ba ta sama za a hau ba. Magudin siyasa da hadamar kudin talakawa duk munayi. Ina tsammanin ma shiyasa Allah Yake jarrabarmu da lalurori da kala kala da 'ya'ya marasa da'a. Yasa hannu ya share hawaye. Ina matukar son Junaid ganinsa nake tamkar mahaifina saboda kamaninsu. Duk abinda ya zama a yau laifina ne saboda yadda na sakar masa yake facaka da kudin talakawan kasar nan. Tun farkon abin mahaifiyarsa ta fara hanawa ni kuma ina ta ganin kamar lokacinsa ne. Maganar tasa sarkewa tayi saboda tari Mal Aminu ya rirrike shi. Sai da abin ya lafa ya cigaba da magana. Muna cikin wani lokaci da yaran da ka tsaya da kyau wurin tarbiyarsu ma baci suke balle wanda aka sakewa. Masifu sunyi mana yawa duk a dalilin nesanta kanmu da mukayi daga Allah da koyarwar Annabi SAW.
Mal Aminu ya dan tabe baki don shima sheda ne akan rashin adalcin kasarnan da  yadda yake ganin tarbiyar yara yanzu a matsayinsa na malamin sakandire. Ji yayi senator ya rike masa hannu wanda hakan ya dan tsorata shi. Sati biyar kenan da likita ya tabbatar min da cewar inada ciwon zuciya kitse ya lullube ta. Babu wanda na fadawa sai ku biyun nan da na hadu daku a yau. Likitan ya tabbatar min ko dai na cigaba da rayuwar shan magani ko na mutu. Subhanallahi Alh Bashir ya fada.
Batul Mamman💖



Post a Comment (0)